A wani labarin kuwa, bisa kokarin bunkasa tattalin arziki, ta fannin noman zamani, hukumar samar da ci gaba, ta kasa da kasa ta kasar Amurka (USAID) ta kaddamar da zuba jarin dala miliyan 60, har na tsawon shekara biyar don zuba jari a fannin kasuwanci a nahiyar Afirka da kuma bunkasa fannin noma a Nijeriya.
A cewar hukumar hakan zai kuma samar da ayyukan yi sama da sababbin ayyuka guda 40,000. Har ila yau, hakan zai kuma taimaka wajen samar da hanyoyin yin kasuwanci a saukake a fanin aikin noma.
- An Nemi Fulani Su Manta Da Bambancin Da Ke Tsakaninsu Don Kubuta Daga Matsalar Tsaro
- Majalisa Ba Ta Da Hurumin Dakatar Da Shugaban Hukumar Zabe Ta Jiha – Shugaban NBA
A jawabinsa a wurin kaddamarwar da aka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja Jakadan Amurka a Nijeriya, Mary Beth Leonard ya sanar da cewa, Nijeriya ta na da kasar yin noma da za a iya zuba dimbin jari mai yawa.
Jakadan Amurka a Nijeriya Mary Beth Leonard ya ci gaba da cewa, muna nunawa bukatarmu ta kara zuba jari a fanonin tattalin arziki da kuma fannin noma a Nijeriya ta hanyar tattaunawa ta kasa da kasa.
Mary Beth Leonard ta ce, a yau muna bikin kara karfafa zuba jari da kuma a fannin kasuwanci, mummman ganin cewar kasar Amurka ta kasance wadda ta zuba jari mai dimbin yawa a Nijeria.
Harkar ta hanyar kasuwancin biyu, ta kai ta dala biliyan 10 a duk shekara.
Babban Sakataren Ma’aikatar Aikin Gona ta Kasa, Dakta Ernest Umakhihe, a jawabinsa a wurin taron ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da damar wajen habaka fannin aikin noma, musamman don su ragewa kawunansu radadin talauci da kuma kara inganta rayuwarsu.
A wata sabuwa kuwa, akwai alamun da nuna cewa, akwai fata nagari a fannin noma Ruber a Nijeriya bayan da masu ruwa da tsaki a fanin suna nuna cewar a shirye suke sufarfado da fannin, inda a jihar Koros Ribas, aka kadadar yin noma15,000 don noman roba a jihar.
Kungiyar masu sarrafa roba ta kasa ce ke shirin yin noman na robar, inda aikin zai kai tsawon shekara10 ana gudanar da shi, wanda ya hada da shuka sabbin irin rubar.
Shugaban ne ya sanar da hakan a lokacin da ya kaddamar da kungiyar ta kananan hukumomi da ke cikin jihar ta Koros Ribas da aka gudanar a garin Kalaba.
Inameti ya ce, kirkiro da kungiyar ya zama wajibi idana aka yi la’akari da irin dimbin mahimmancin da noman roba ke da shi.
Ya ce, gaba da cewa, a bias la’akarin da aka yi na ganin masu ruwa da tsaki a jihar ta Koros Ribas sun mayar da hankali kan farfado noman rubar a jihar, ya sa gwamnati za ta ba su gudummawa domin kara musu karfin gwiwar yadda za su fadada noman nasu, da kuma samuncin moriyar abin da suka noma.
Hakan zai sa su kara samun karfin gwiwa wajen ci gaba da fadada wannan noma. Sannan kuma hakan zai taimaka wajen samun sabbin manoman da za su runguni wannan noma na roba.