A halin yanzu ‘yan bindiga suna neman Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansar yara 20 da suka yi garkuwa da su a Kusherki, karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja.
Mutanen da aka sace kimanin makonni uku da suka gabata, har yanzu suna hannun wadanda suka sace su.
- Kamfanin Sin Ya Haskaka Kauyen Lauteye Na Jihar Kanon Nijeriya
- El-Rufai Ya Bayar Da Umarnin Mayar Wa Dalibai Kudadensu Na Makaranta Da Aka Karba
Alhaji Auwal Usman daga Kusherki ya bayyana cewa a halin yanzu ‘yan bindigar na neman Naira miliyan 40 kafin su sako yaran da suka yi garkuwa da su da ke fuskantar mawuyacin hali a hannun ‘yan bindigar.
Wadanda aka yi garkuwa da su da suka hada da maza hudu da mata 16, dukkansu ‘yan shekaru hudu ne da kuma 10.
Usman ya yi kira da a kara himma da gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an ceto su ba tare da wani ya samu rauni ba.
“Muna kira ga gwamnatin Jihar Neja da jami’an tsaro da su kawo mana dauki domin iyayen yaran da aka sace suna fuskantar matsananciyar matsin lamba sakamakon sace ‘ya’yansu,” in ji Usman.
A nasa jawabin kwamishinan tsaron cikin gida da ayyukan jin kai, Emmanuel Bagna Umar, ya bada tabbacin gwamnatin jihar ta kuduri aniyar kawar da duk wani nau’in laifuka a jihar.
Ya kara da cewa gwamnati na aiki tukuru tare da hadin gwiwar rundunonin kasa da kasa domin kubutar da yaran da sauran wadanda aka yi garkuwa da su a fadin jihar tare da tabbatar da cewa sun dawo wurin ‘yan uwansu a raye ba tare da an samu matsala ba.
Umar ya ci gaba da cewa: “Duk da cewa jihar na samun asarar rayuka, amma a gaskiya muna samun nasara a yakin da ake yi da ‘yan bindiga. Muna jinjina wa jami’an tsaro da kungiyoyin ‘yan banga a jihar kan yadda suke gudanar da ayyukansu.”