Rundunar Sojin Sama ta Operation Hadarin Daji ta kawar da wasu jiga-jigan ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo, Halilu Buzu, a Jihar Zamfara da Alhaji Ganai da abokinsa Yellow Kano a Jihar Kaduna.
A cewar majiyae sojin, an kashe ‘yan ta’addan da mayakan ne a wasu hare-hare ta sama guda biyu biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu.
- Yawan Adadin Mutane A Fadin Duniya Ya Doshi Mutum Biliyan 8 — MDD
- 2023: Ko Takarar Gwamnan Kano Ta Yi Wa Sadiq Aminu Wali Girma?
An kashe Halilu Buzu ne a ranar 21 ga watan Oktoba, 2022 a yayin wani harin da aka kai musu ta sama a sansaninsu da ke karamar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.
Wani babban jami’i ya ce an ba da izinin kai harin ta sama ne bayan wasu bayanan sirri da aka samu sun nuna cewa wani kasurgumin dan ta’adda mai suna Halilu Buzu da ke garin Sububu a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara ya shirya ganawa da wasu daga cikin sojojin da ke yankin.
Hukumar leken asirin ta kuma bayyana inda da kuma ainihin wurin da yake ajiye kayan aikinsa inda shi da tawagarsa suka saba ajiye harsashi da ababen hawa.
“Saboda haka, jiragen yaki NAF sun kai farmaki a lokaci guda inda taron ya gudana da kuma cibiyar hada kayan aiki.
“An hangi wata wuta ta tashi bayan kai harin, lamarin da ke nuni da cewa akwai yuwuwar wurin ya kunshi wani abu mai zafi,” in ji jami’in.
Majiyar ta ce binciken da aka yi a kan barnar shanu ya nuna wurin da taron ya gudana da kuma wurin da aka a lalata.
Ya ce bayanan da aka samu a baya-bayan nan sun nuna cewa lallai an kawar da Halilu Buzu a harin da aka kai ta sama tare da wasu shugabannin ‘yan ta’adda.
Ya kara da cewa, “Kawar da Halilu Buzu ya zo ne a matsayin abun farin ciki ga mazauna yankin Sububu, Anka (Bayan Daji) da kuma mahadar Bayan Ruwa a Jihar Zamfara bisa la’akari da kwarewarsa wajen ta’addanci da azabtar da wadanda yake yin garkuwa da su, tuni rashinsa ya rage yawaitar faruwar kai hare-hare da garkuwa da mutane, satar shanu da sauran ayyukan ta’addanci a yankin.”
Ya ce an kai irin wannan harin ta sama a ranar 14 ga watan Nuwamba, 2022 a wani wurin da wani kasurgumin dan ta’adda yake a unguwar Alhaji Ganai a dajin Kidandan da ke karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Ya ce harin ta sama ya zama wajibi ne bayan da hukumar leken asiri ta sa ido da bin diddigi, da kuma gano yadda al’amuran Alhaji Ganai da dakarunsa ke a wurin.
“Bayanan sirri sun nuna cewa an lalata wasu gine-ginen da ke wurin da suka hada da gidan Alhaji Ganai da babura, sannan an kashe ‘yan ta’adda da dama da suka hada da Yello Kano, na hannun damar shugaban ‘yan ta’adda, Musa Balejo da wasu kasurguman ‘yan ta’adda bakwai bayan harin,” a cewarsa.