Ministan ma’aikatar noma da raya karkara Dakta Mohammed Mahmood Abubakar ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya na aiki da hukumar yaki da fasakwari domin a dakile shigo da abinci daga kasashen ketare zuwa cikin kasar nan.
Dakta Mohammed ya sanar da hakan ne a jawabinsa yayin ziyarar aiki da ya kai a shalkwatar cibiyar binciken ‘ya’yan itatuwa (NIHORT) da ke garin Ibadan cikin jihar Oyo.
- Ra’ayoyinku A Kan Batun Hako Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe
- Abokai Na Zahiri Suna Zurfafa Huldar Zumunci A Sabon Zamani
A cewar Dakta Mohammed, a cikin shirye-shiyen da gwamnatin tarayya ke kan yi domin ta tabbatar Nijeriya ba ta fuskanci karancin abinci ba, ma’aikarar ta fara shirin fara gudanar da aikin noman rani wanda za a fara a cikin wata mai zuwa, inda ya yi nuni da cewa, fannin aikin noma shi ne na daya da ke kara habaka fannin tattalin arzikiin kasar nan.
A cewar Dakta Mohammed,“Zamu tabbatar daukacin hukumomin gwamnati na yin aiki kafada da kafada da hukumar kwastam da muke yin aiki da su, kamar hukumar kwastam domin a tabbatar ba a shigo da abinci ta barauniyar hanya zuwa cikin kasar nan ba domin ba ma son mu samu karancin abinci a kasar nan, inda ya kara da cewa, a yanzu ba ma karancin abinci a kasar nan, muna da wadataccen abinci.
Ministan ya sanar da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na bai wa ma’aikatar taimakon da ya dace, domin yana taimaka wa fannin aikin noma ta bayar da gagarumar gudunmowa wajen kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya, inda kuma ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba kara kara bayar da gudunmawa domin cibiyar ta kara fadada gudanar da binciken don a kara bunkasa fannin oma a kasar nan.
“A yanzu ba ma karancin abinci a kasar nan, muna da wadataccen abinci a kasar nan”.
A taron, Dakta Mohammed ya kuma mika ingantacen irin Kubewa da cibiyar ta NIHORT ta samar gaingantaccen ga sashen bunkasa aikin noma (ADPs) da kuma ga wakilin kungiyoyi masu zaman kansu dake suka fito daga jihohin Oyo, Osun da Ogun.
A na sa jawabin tunda farko, shugaban cibiyar NIHORT Dakta Muhammed Attanda ya godewa ministan, musamman bisa taimakon da cibiyar ke ci gaba da samu daga ma’aikatar noma, inda ya ce, cibiyar ta gudanar da hakan ne domin jin ta bakin manoman a kan irin ingancin irin noma da cibiyar ke samar wa manoman.
Dakta Attanda ya kara da cewa, wannan aiki ne da cibiyar ta saba gudanar wa duk shekara, muna kuma kiran aikin a matsayin yin nazari dangane da irin binciken da cibiyar ta gudanar a fannin aikin noma, musamman domin mu ji ra’ayoyin manoman a kan irin noman ga cibiyar ta samar.
“Cibiyar ta gudanar da hakan ne domin jin ta bakin manoman a kan ingancin irin noma da cibiyar ke samar wa manoman”.
A na sa jawabin, shugaba kungiyar bunkasa noman mknoma ta kasa reashen jihar Oyo (ADFA) Alhaji Salihu Imam ya yaba wa cibiyar ta NIHORT kan taimaka wa manoma, inda ya yi ikirarin cewa, cibiyar ce kadai, da ta samar wa da manoman da kadada daga 30 zuwa 40 don yin noma ba tare da biyan wani kudin hayar gona ba.
“Cibiyar ce kadai, da ta samar wa da manoman da kadada daga 30 zuwa 40 don yin noma ba tare da biyan wani kudin hayar gona ba”.
Ita ma jami’ar shirin na JDPC ta reshen garin Ibadan, uwargida Adebola Ojewale, wacce kuma tana daya daga cikin wadanda suka amfana ta nuna jin dadinta akan amfanar da suke yi da cibiyar.
Adebola Ojewale ta sanar da cewa,” Na ji dadi matuka domin ko a kwanan baya, manoma na sayo irin noman ne a kasuwanni wadanda akasarin irin, ba shi da ingancin da ake bukata, amma ina da yakinin ganin cewa wamnan irin ya fito ne daga cibiyar, ba ni da wata tantama a kansa”.