A lokacin da ‘yan takara suke ci gaba da gudanar da yakin neman zabe domin tallata manufofinsu da za su iya saye zukatan masu jefa kuri’a, kungiyoyi daban-daban suna kokarin ganawa da ‘yan takarar ta yadda za su amfani magoya bayansu idan suka hau kan karagar mulki.
Kungiyar kiristocin Nijeriya (CAN) ta gayyaci ‘yan takarar shugaban kasa domin ganawa da su da kuma bayyana musu irin muradanta ga duk wanda ya samu nasarar zama shugaban kasa a 2023.
- CMG Ya Lashe Lambobin Yabo 4 Na Watsa Shirye-shirye Na Gasar Wasannin Olympics Ta Beijing 2022
- 2023: Barazanarka Ba Za Ta Ba Mu Tsoro Ba – Martanin Magoya Bayan Atiku Ga Wike
Da yake jawabi ga ‘yan takarar, shugaban kungiyar CAN, Archbishop Daniel Okoh ya bayyana cewa Nijeriya tana fuskantar matsalolin shugabanci. Ya dai daura alhakkin matsalolin ne da rashin amfani da tsarin mulki yadda ya dace.
Ya kara da cewa CAN ta tauki lokaci mai tsawo wajen gudanar da nazari kan matsalolin da ke addabar kasar nan tare da lalubo hanyar dinke bakin zaren.
Okoh ya ce, “Mun shawarci ‘yan Nijeriya kan matsalolin rabuwar addinai da kabilanci da zamantakewa a kasa, sannan muka samar da kundin da zai iya magance wadannan matsaloli.
“Kundin ya mayar da hankali ne kan matsalolin siyasa da zamantakewa da tattalin arziki. Kundin ya bayar da cikken shawarwari na yadda za a magance matsalolin da Nijeriye ke fuskanta wadanda suka hada da adalci, daidaito ga dukkan kabilu da addinai da daidaita rabon arzikin kasa da samar da ‘yancin siyasa da dai sauransu.”
A cewarsa, akwai bukatar tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasa da fahimtar juna kan abubuwan da suka shafi kiristocin Nijeriya da kuma samar da wani tsari da za a iya magance su.
A cikin ‘yan takarar da suka halarci ganawar sun hada da na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha da na APC, Asiwaju Bola Tinubu da na PDP, Atiku Abubakar da kuma na LP, Peter Obi.
Kungiyar CAN ta zayyana wa ‘yan takarar shugaban kasan sharudda wadanda suka hada da samar da tsarin ‘yansandar jihohi da raba karfin iko a tsakanin jihohi da daidaita dukkan addinai da bai wa dukkan kungiyoyin kabilu ‘yanci da barin damar mallakar albarkatun ga al’ummar wuri ciki har da ruwa da dazuka da dakatar da kiwo da daidaita makamai a cikin majalisar zantarwa da sauran makaman siyasa da bari kowacce kabila da addini ta kasance tana da mukami a rundunar sojojin Nijeriya da sauran ma’aikatun tsaro da kuma bai wa dukkan ‘yan Nijeriya kulawa da lafiya kauta.
Tinubu ya bayyana wa CAN cewa zai daidaita dukkan ‘yan Nijeriya tare da bayyana matarsa a matsayin kirista da kuma ‘ya’yansa. Ya sha alwashin cewa zai dunga tuntubar CAN kan batutuwan da suka shafi kasa idan har ya samu nasarar zama shugaban kasa.
Hakazalika, gamayyar kungiyoyin arewa wadanda suka hada da na dattawan arewa na ACF da na NEF da ARDP da ABF da Jamiyyar Matan Arewa sun samu nasarar tattaunawa da wasu daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyu daban-daban.
Gamayyar kungiyoyin sun bayyana cewa a halin yanzu arewa tana bukatar samun shugaban kasa da zai iya magance matsalilin yankin da kuma kasa baki daya.
A cewar kakakin NEF, Dakta Hakeem Baba-Ahmed an gudanar da wannan yunkuri ne domin fahimtar abubuwan da ‘yan takarar za su yi wa arewa. Ya ce za su mara baya ne ga duk dan takarar da ke da manufa mai kyau da tunani mai kyau ga arewa da ma Nijeriya gaba daya ba tare da la’akari da yankinsa ba ko addininsa.
Ganawar ta gudana ne a dakin taro da ke Arewa House a Kaduna, inda cikin ‘yan takarar shugaban kasan har da Kola Abiola na jam’iyyar PRP da Prince Adewale Adeboye na jam’iyyar SDP da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar LP da kuma Bola Tinubu na jam’iyyar APC duk sun gurfana a gaban gamayyar kungiyoyin arewa.
Wannan wata dama ce ga ‘yan takarar wajen tallata kansu domin samun kuri’un ‘yan arewa. Yankin yana da dinbin mutane wanda mafi yawancin ‘yan siyasa idan suka lashe zabe sai su yi watsi da yankin.
Gamayyar kungiyoyin dattawan arewa sun bayyana cewa makasudin shirya wannan tattauwana shi ne, ganawa da ‘yan takarar shugaban kasa na zaben 2023 domin jin yadda za su magance matsalolin da suka addabi yankin arewa da ma Nijeriya gaba daya.
Cikin matsalolin da yankin arewa ke fuskaskanta sun hada da rashin tsaro da rarrabuwar kawuna da rashin daidaituwar al’amura da masu tayar da kayan baya da sauran kalubale na zamandakewa da suka addabi yanki da ma Nijeriya gaba daya.
A sai kuma a cikin muradun CAN da na dattawan arewa akwai inda suke da kamanceceniya wadanda suka hada da maganci matsalolin tsaro da rarraba madafun iko da bai wa ‘yan Nijeriya kakkawan kulawa da gudanafr da shugabanci nigari ga duk wanda ya zama shugaban kasa.
Akwai kuma inda muradan suka saba wa juna wadanda suka hada da hana kiwo da mallakar albarkatun kasa ga al’ummomin yanki da bai wa kogiyoyi ‘yancin da samar da ‘yansandar jihohi da dai sauransu.
Tun da farko dai, kungiyar CAN ta kyamaci tikitin takarar musulmi da musulmi, musamman ga jam’iyya mai mulki, sai kuma daga baya ta bayar da kai buri ya hau, inda har ta gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki tare da tabbatar masa cewa za ta iya mara masa baya matukar ya samu nasarar cika sharuddan da ta ginda ya masa.
Da yake fashin baki a kan wannan lamari ga LEADERSHIP Hausa, Malami a sashin koyar da harsuna na Jami’ar Sojoji da ke Biu a Jihar Borno, Ibrahim M. Baba ya bayyana cewa, abubuwan da kungiyoyin biyu suka ayyana alamu ne na an fara farkawa daga barci a bangaren siyasa a Nijeriya. Yana mai cewa kasashen da suka ci gaba ana zaban ‘yan takara ne da irin kyawawan manufofi da tsare-tsaren da suka iya gabatar wa jama’a, don haka ne ya ce da irin wannan matakin na jero wa ‘yan takara muhimman abubuwan da jama’a suke so, zai kara kusanto da jama’a da gwamnati da kuma rungumar ayyukan ci gaba da aka musu dari bisa dari tare da kulawa da su.
“Wannan matakin ya nuna maka cewa Nijeriya muna kara tasowa domin hawa kan turbar dimokuradiyya madaidaiciya kenan sabanin yadda muke yin abubuwa a da baya. Domin in ka duba a tsarinmu na dimokuradiyya ya bambanta da sauran kasashen da suka ci gaba wadanda suke gudanar da dimokuradiyya bisa tsari.
“Wannan ya gwada cewa mutanenmu sun fara wayewa kuma sun fahimci cewa yana da kyau a zauna a tattauna da dan takara a fada masa abubuwan da jama’a ko mutane suke so kafin ma a kai ga zabinsa.
“Kuma shi ma ya fada kudirorin da yake son aiwatarwa idan ya ci zabe, wannan shi ne muke kira dimokuradiyya daga tushe. Rashin yin hakan a baya shi ne ya janyo ka ga gwamnati ta gudanar da abubuwa da dama, amma mutane ba su damu da su ba.
“To ka ga ta hanyar irin wannan zai sanya su kansu al’umma su samu dama na gabatar da koke-kokensu ga masu neman tsayawa takara, domin in sun hau su san abubuwan da za su sanya a gaba,” a fadin malamin.
Ibrahim M. Baba ya ce maganganun da kungoyin nan suka gabatar wasu na da muhimmanci wasu kuma akasin hakan, ya nuna cewa wasu bukatun cike suke da surkulle domin kuwa babu tunani ko kadan a cikinsu.
“Yanzu mu dauki bukatu 11 da CAN ta gabatar wa ‘yan takaran nan… Su kansu sun yi tufka sun yi warwara, yanzu ka ga misali ka dauki shi kansa maganar samar da ‘yansandan jihohi din nan abu ne wanda in ka kalli yadda muke a Nijeriya ba abu ne wanda za a ce za a gindaya sharadi wa dan takara da shi ba, saboda jihohin nan a yanzu haka ba sa iya rike kansu, wanda a yanzu haka akwai jihohi da dama da ke fama da matsalar biyan albashin ma’aikatan jiharsu. Yanzu idan aka ba su dama su kirkiri ‘yansandan jihohi ta ina kake tunanin za su iya biyan su? Ka ga wani karin nauyi ne da za a dora wa gwamnatocin jihohi.
“Idan ba ka manta ba wannan gwamantin ta Shugaba Muhammadu Buhari kusan sai da ta rika ba da tallafin kudin fansa ga jihohi ‘BAILOUT’ (a dauki kudi a ba ka aro don ka samu ka cika ka biya albashi da sauransu) duk da an yi hakan har yanzu akwai jihohi da dama a nan arewa ana bin su bashin albashi ko fansho da sauran matsaloli.”
Ya ce illar samar da ‘yansandan jihohi ba ma a nan kawai ta tsaya ba, “Ka ma dauka cewa gwamnonin za su iya biyan albashin nan idan suka dauki ‘yansandan jihohi, illar hakan ya wuce yadda kake tsammani. Kai-tsaye idan aka ce wasu gwamnonin na da ikon juya ‘yansanda a hannunsu tamkar an ba su damar musguna wa abokan hamayyarsu a siyasance ne ko a bangagaren rayuwa. Yanzu ma haka da ake amfani da ‘yansandan gwamnatin tarayya ai gwamnoni suna iya amfani da su wajen musguna wa abokan hamayyarsu, kowa ya san da hakan.
“To idan aka ware wa gwamnanoni wasu ‘yansandan jihohi matsalolin za su ninku kuma lallai ba ci gaba da za a samu ba. Ya kamata mu duba matakin ci gabanmu kafin bijoro da maganganu.
“Abu na biyu bukatar da suke da ita ta samar da daidaito kan addinai da bai wa kungiyoyin kabilu ‘yanci, eh, haka ne yana da kyau kowani dan kasa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar ya zama an ba shi hakkinsa kamar yadda aka bai wa kowani dan kasa. To, amma a gefe guda kuma daga cikin abubuwan da kungiyar CAN suke nema wai shi ne a dakatar da tsarin gina RUGA kuma wai a bai wa mutane damar su mallaki dazuka da magudanan ruwa da sauransu, wannan maganar ta dakatar da kiwo ka ga wani tufka da warwara ne.
“Ta yaya za a yi ku ce kuna gwagwarmayar neman kowace kabila a ba ta ‘yancin kashin kanta amma a gefe guda kuma kun zo kun ce za a dakatar da kiwo a wasu dazuzzuka, kamar kun tauye wa wasu hakkinsu alhali kiwon nan akwai wasu al’ummomi da tun a al’adance sun taso ne da kiwon dabbobi da yin noma kafin su samu abincin da za su ci, kuma su ma ‘yan kasa ne da suke da ‘yancin da za su yi rayuwa a kowani a fadin kasar nan, kun zo kun ce ka da a barsu su yi kiwo, to me hakan yake nufi?
Dangane da batun daidaita mukaman siyasa ko raba mukamai da suka shafi gidan soja da sauran ma’aikatun tsaro da CAN ta gabatar, Malamin ya ce, “Ai daman babu bambancin da ke nuna wa wani addini ko kabila. Kusan yanzu ina ganin a dukkanin ma’aikatu babu inda aka tsaya a kan bin tsarin aiki na cewa mutumin da ya cancanta, ya kware a bangaren aiki, ya kware a bangaren gudanar da al’amura da mulki shi kadai ne ya kamata a dauko a ba shi jagoranci in ba a gidan soja ba. Mu gaskiya ba mu gurbace ta yanda har za a ce don addininka shi ne zai sanya a dauki wani mukami a baka ba.
“Idan ana irin haka a sauran bangarorin siyasa za mu iya cewa haka ne, amma a maganar bangaren aikin soja gaskiya babu wata wariya da ake nunawa. Jajircewarka da abun da ake kira ‘na gaba’ mataki-mataki suke bi, ba zai yiwu kawai a dauko ka kana karamin ma’aikaci kawai a ba ka baban wuri a ce za ka shugabanta ba. Akwai mataki-mataki da sai ka taka, wannan matakin ne zai nuna cewa mutum ya cancanci in aka daurashi a wuri kaza to zai iya rikewa.
“Ita kungiyar CAN ya kamata ta sake duba wadannan abubuwan sosai. Haka suka taba yin wani tufka da warwara kwanaki, suka ce suna sukar cewa fitar da ‘yan takara guda biyu shugaba da mataimakinsa su fito daga cikin addini daya, suna Alla-wadai, sannan an zo maganar tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasa kun kira shi wannan dan takara da yake cikin jam’iyyar da suka fitar da musulmai biyu a matsayin ‘yan takaransu, ka ga wannan ma yin amai ne da lashewa.
“Tun da farko ma bai kamata su zauna suna sukar don an kawo ‘yan takara biyu daga addini daya ba, wannan bai zama matsala a tsarin dImokuradiyyarmu ba, kuma a da baya can an yi irin wannan. In ban da ma lalacewar abubuwa bai kamata addininka ya zama maka tarnaki ga neman takara ba, domin kai ka zo ne za ka yi rantsuwa da cewa za ka yi mulki tsakani da Allah ba tare da nuna wariya ba. Saboda haka ba abu ne da ya shafi addininka ko kabilarka ba. Abu ne da ya shafi al’ummar Nijeriya wanda ya kamata ya zama ka mutunta littafan da ka rantse da shi.”
Daga bisani malamin ya dora muradun bangaron biyu na CAN da Dattawan Arewa a sikeli inda ya ce, akwai wuraren da suka hadu kamar wajen samar da ilimi, tattalin arziki da inganta tsaro dukkaninsu abubuwa ne da ake bukata.
M. Baba ya ce, yawancin bukatun dattawan arewa sun dace da manufar kowa, lura da cewa suna neman a shawo kan matsalolin da suka yi wa arewacin kasar nan katutu ne da suka kunshi matsalar tsaro, samar da ayyukan yi, bunkasa tattalin arziki da dai sauransu, kusan hakan ma yana daga cikin manufofin da ‘yan takaran suka zo da su.
“Babbar ma barazana a dimokuradiyyar Nijeriya su kansu wadannan ‘yan takaran idan sun zo sun yi alkawura ba cikawa suke yi ba. Wadannan abubuwan da kungiyoyin suka jero musu har su ce sun amince ba lallai ba ne idan sun ci kuma su aiwatar da su ba. A baya-bayan nan hakan ya faru a gwamnatin da ke ci ta Shugaba Buhari, alkawura da dama da ya zo ya yi yakin neman zabe da su da dama kuma gwamnatinsa ta kasa cika su..
“Buhari kafin ya hau ya yi alkawarin cewa zai tabbatar da yin aikin wutar Mambila, amma ka ga daga karshe an zo an ce ba a ma yi maganarsa ba. Maganar tattalin arziki kuwa za a sanya talaka walwala a cire shi daga cikin kungin tsadar rayuwa, ka ga duk wadannan abubuwan an yi kamfen da su amma da gwamnatin ta samu nasara ba su aikata ba. Ni dai fatana shi ne duk alkawuran da dan takara ya yi ya ji tsoron Allah ya cikasu.”
A bayana dai, CAN ta bayyana cewa kiristoci a dukkan yankunan kasar nan za su yaki duk wata jam’iyya da ta bayar da tikitin musulmi da musulmi, idan ta ce hakan ya saba wa ‘yancin addini da kuma zaman lafiyar Nijeriya.
Haka ita ma cocin Katolika ta Nijeriya ta kyamaci takarar musulmai guda biyu, inda ta ce babbar barazana ce ga hadin kan kasa a tsakanin mutane. Ta kara da cewa ba za ta taba goyan bayan duk wata jam’iyyar siyasa da ta amince da takarar musulmi da musulmi ba, domin zai iya ruguza zaman lafiya a kasar nan.
Amma daga bisani CAN ta sassauta ra’ayinta kan takarar musulmi da musulmi da jam’iyya mai mulki da amince da shi, wanda ta dage wajen magance matsalolin Nijeriya.
Bugu da kari, CAN ta dage a kan dole a hana kiwo wanda ta ce shi kadai ne hanyar da zai samar da zaman lafiya ga al’ummominta. Ta ce a hana kiwo tare da zamanantar da kowon dabbobi wajen habaka tattalin arziki.
Kungiyar CAN da ce idan har aka amince da wannan sharruda da ta gindaya, to shi zai magance matsalolin da kasar nan take fuskanta a halin yanzu.
Yayin da gamayyar kungiyar dattawan arewa take ganin a bayan an yi musu sakiyar da babu ruwa wanda a yanzu ya zama wajibi su titse ‘yan takarar shugaban kasan, domin ganin sun zabi dan takarar da zai iya magance matsalolin arewa. A cewarsu, ta wannan hanya ce kadai mafita ga yankin arewa da kuma Nijeriya gaba daya.