Sakamakon binciken da aka gudanar kan zargin mallakar katin zabe ba bisa ka’ida ba, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta samu nasarar gano kayayyakin zabe a gidajen wasu mutane ciki har da ‘yan siyasa.
An dai samu wannan nasara ce bayan da jami’an tsaro suka kai samame jim kadan da samun rahoton zargin, inda aka gano katin zabe da aka boye a ramuka a wasu sassan kasar nan. Wannan lamari ya tabbatar da zargin da ‘yan Nijeriya suke yi game da kokarin yin magudi a zaben 2023.
- Shugaban Rikon Kwarya Na Chadi Na Son Zurfafa Hadin Gwiwa Tare Da Sin
- Aisha Buhari: Kungiyar Daliban Nijeriya Za Ta Gudanar Da Zanga-Zanga Kan Cafke Aminu
A watannin da suka gabata ne ake ta yada wani faifen bidiyo a kafafan sadarwa da ke nuna yadda wasu suka boye daruruwan katin zabe a karkashin rami a bola da ke kan hanya.
INEC ta tabbatar da zargin a wannan lokaci, inda ta bayyana cewa ta samu rahoto kan lamarin katin zabe kuma ta sanar da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro domin gudanar da bincike tare da daukan mataki.
Haka kuma hukumar ta tabbatar da cewa za ta bayyana wa mutane sakamakon binciken da aka gano idan an kammala.
Sakamakon binciken hukumar zabe ta kai ga gurfanar da Nasiru Idris a kotun majastiri da ke Sakkwato kan samun sa da katin zabe har guda 101, wanda aka yanke masa hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekara guda.
Haka kuma, rundunar ‘yansanda a Jihar Kano ta samu nasarar damke wani mutum da katin zabe har guda 367. An dai gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu kuma hukumar zabe za ta ci gaba da bibiyan shari’ar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin hukumar INEC, Festus Okoye ya bayyana cewa laifin ya zaba wa sashi na 117 da 145 na dokar zaben 2022. Ya ce rundunar ‘yansandan Nijeriya ta samu nasarar kama wasu mutane sakamakon mallakar katin zabe ba bisa ka’ida ba a wasu jihohin kasar nan.
Bisa bayanan da LEADERSHIP ta samu, Okoye ya ce, “A bangare daya, ‘yansanda sun kammala bincike tare da mika lamarin ga hukumar zabe sakamakon, inda aka tabbatar da kama Nasiru Idris da katin zabe 101 lokacin da aka gurfanar da shi a gaban kotun majastiri da ke Sakkwato, wanda laifin ya saba wa sahi na 117 da 145 na dokar zaben 2022. An dai yanke masa hukuncin daurin shekara guda a jidan yari.
“Shi kuma wanda aka kama da katin zabe 367, hukumar INEC ta gurfanar da shi a gaban kotu, sannan hukumar za ta ci gaba da bibiyan shari’ar tare da sauran wadanda suka karya dokar zabe ta yadda za a hukunta su daidai da laifin da suka aikata.”
A watan Yulin wannan shekarar, an samu nasarar gano daruruwan katin zabe a cikin magudanar ruwa a yankin Rumuodara da ke karamar hukumar Obio-Akpor a Jihar Ribas.
Mazauna rukunin gidajen Apa-Ogwu da ke yankin Rumuodara sun firgita lokacin da aka gano katin zabe har guda 10,000 a cikin lalataccen magudanar ruwa. An dai samu nasarar gano katin zaben ne lokacin da mazauna yankin suke share magudanar ruwan.
Bayan makonni uku da gano katin zabe har guda 10,000 a magudanar ruwa a Jihar Ribas, mafarauta sun sake gano guda 300 a cikin jaka a cikin wani kango da ke kan hanyar AIT/Elebele a garin Yenogoa cikin Jihar Bayelsa.
Haka kuma an sake gano katin zabe a Jihar Imo a karkashin kasa tare da hotunan wani mutum.
Da yake mayar da martani kan rahoton kama mutane da daruruwan katin zabe, dan majalisar wakilai, Hon Mark Gbilah ya bayyana cewa dole ne ‘yan Nijeriya su nuna damuwarsu kan na’urar zabe da INEC za ta yi amfani da shi da kuma sauran shirye-shiryen hukumar.
Dan majalisan da ke wakiltar Gwer ta yamma da kuma Gwer ta yamma da ke Jihar Benuwai a zauren majalisa ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce ya kamata hukumar INEC ta kulla kawance da jami’an tsaro kan gudanar da binciken gaggawa idan aka samu irin wannan lamari.
Haka kuma, cibiyar bunkasa dimokuradiyya (CDD) ya yi kira ga INEC ta kula wajen yin amfani da na’urar bayyana sakamakon zabe. A cewarta, katunan zai kasance bai da amfani a wurin mutane da suka mallaki katin zabe mai yawa sakamakon yin amfani da na’urar zabe.
CDD ta ce INEC tana kan hanya madaidaiciya wajen dagewa kan amfani da na’urar a zaben 2023.
Babban mai gudanar da shirye-shirye na CDD, Austin Aigbe shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da Jaridar LEADERSHIP a Abuja. Ya ce na’urar zabe za ta kasance mai matukar wahala ga masu amfani da katin zabe masu yawa.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya su kai rahoton duk wani wanda aka samu da katin zabe masu yawa.
“Ina tunanin sakamakon kin amfani da na’urar zabe ne ya sa aka kasa samun sahihin zabe a 2019, amma idan an yi amfani da shi a wannan karo za a samu sahihin zabe wanda mutane za su amince da shi,” in ji shi.
Wakilin Nijeriya a kungiyar daliban Afirka (ASUP), Kwamared James Uneze ya bayyana cewa suna da gwarin gwawa kan shugaban INEC da hukumar na gudanar da sahihin zabe. Uneze ya yi kira ga INEC ta karfafa tsaro a dukkan ofishoshinta da ke fadin kasar nan.
Ya ce wadanda ke mallakar katin zabe da yawa ya kamata su sani ba za su amfana da komi ba, domin INEC za ta gudanar da zaben 2023 ne ta hanyar amfani da na’urar bayyana sakamakon zabe, wanda dole kowani mai jefa kuri’a za a dauki zanen hannunsa. Ya ce na’urar za ta taimaka matuka wajen rage magudin zabe.