Shekara 8 kenan ya rage zuwa 2030, shekarar da al’ummar duniya ta sha alwashin kawo karshen cutar nan mai karya garkuwan jiki (AIDS), wanda aka fi sani kanjamau amma har yanzu Nijeriya na fuskantar manyan matsaloli da ke haifar da banbanci da rashin daidato a tsakanin masu fama da cutar wanda hakan zai kawo cikas a wannan hakoron na kawo karshen cutar a duniya.
A daidai lokacin da Nijeriya ta tabbatar da matsayin kashi 90 na mutanen da suke fama da cutar amma sauran kashi 10 na nan a cikin wani mummunan hali saboda rasahin tantance su tare da sanin halin da suke ciki.
Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya sanar da cewa, lallai Nijeriya ta samu gaggarumin nasarar tabbatar da halin da mutane fiye da kashi 98 na masu fama da cutar ta hanyar tantance su yayin da kuma a halin yanzu fiye da kashi 98 na masu cutar suna karbar magani a cibiyoyi daban daban a sassan kasar.
Ya ce, kashi 98 na masu karbar maganin suna samun saukin da ake bukata.
Amma duk da wannan kokarin har yanzu akwai kalubale da dama da suka shafi al’adu dana zamantakewa da suke haifar da tarnaki a wajen yi wa masu cutar gwaji, ana kuma kokarin cigaba da baiwa masu cutar magunguna a duk inda suke tare da wayar da kan al’umma donh su fito a yi musu gwaji.
A nasa tsokacin, Shugaban Kungiyar masu fama da cutar Kanjamau A Nijeriya (NEPWHAN), Abdulkadir Ibrahim, ya sanar da cewa, nuna kyama da ake yi wa masu cutar yake hana su fitowa a yi musu gwaji da ziyartar asibitoci don neman magani.
Ya nuna damuwarsa a kan yadda ake nuna kyama ga masu cutar kanjamau wanda hakan yake sa masu cutar ke kauracewa asibitoci don karbar maganin da ke bayarwa kyauta.
Ya kara da cewa, “Da zaran cutar ta kama ka amma saboda yadda ake kyamarka ka kasa zuwa asibiti karbar magani jikin ka na iya haifar da wasu sinadarai da za su hana maganin aiki gaba a jikin ka abin da kuma zai haifar da wahallahalu masu yawa ga mai cutar.
“Wannan matsalar zai sa kanjamau ya cigaba da yaduwa a tsakanin al’umma wanda hakan kuma zai haifar da cikas ga kokarin kawo karshyen cutar nan da karshen shekarar 2030.”
Ya lura da cewa, lallai akwai wariya na matsayi a tsakanin al’umma amma kuma akwai tsananin bukatar kowa da kowa ya bayar da nasa gudummawar wajen ganin masu fama da cutar sun samun maganin da ya kamata a lokacin da ya kamata.
Sai dai ya bayyana cewa, lallai Nijeriya tana samnun nasara a kan yaki da cutar kanjamau ta hanyar dora masu fama da cutar a kan tsarin karbar magani amma ta yi matukar gazawa wajen tabbatar da sun cigaba da karbar maganin, ta kuma gaza wajen dora sabbin masu cutar a kan tsarin karbar magani.
Haka kuma kididdiga sun nuna cewa, Nijeriya ta yi nasara matuka a yaki da cutar kaunjamau musamman ganin kusan kashi 90 na masu fama da cutar sun san matsayinsu yayin da kuma kashi 98 ke karbar magani.
Shugaban Hukumar Kula da Yaduwar Cutar Kanjamau ta Kasa (NACA), Dakta Aliyu Gambo, ya ce, za a iya ganin nasarar da Nijeriya ta samu a yaki da cutar kanjamau ne in aka lura da cewa, yaduwa cutar ya matukar raguwa daga yadda yake a kashi 3.4 a shekarar 2017 zuwa kashi 1.3 a shekarar 2018.
Ya kara da cewa a karshen watan Satumba na shekarar 2022, a kasar nan akwai mutum 1,619,133 da ke karbar magani a asibitocin daban daban a tarrayar Nijeriya wanda hakan ke nuna kashi 98 na mutane da ke fama da cutar ke nan a kasar nan.
Ya kara da cewa, sabbin wadanda suka kamu da cutar ya matukar raguwa daga mutum 103,404 a shekarar 2019 zuwa mutum 92,323 a shekara 2021.
“An samu karuwar wuraren da ake karbar magani daga guda 251 a shekara 2007 zuwa 2,262 a shekarar 2020. Sabbin masu fama da cutar sun ragu daga mutum 103,404 a shekarar 2019 zuwa mutum 92,323 a shekarar 2021.
Yadda aka samu karuwar al’umma ya haifar da karuwar cibiyoyin bayar da magungunan kanjamau din inda ya tashi daga cibiyoyi 10 a shekarar 2017 da ke kula da mutum 16,147 zuwa 118 a shekarar 2021 da ke kula da mutum fiye da 221,010,” in ji shi.
Shugaban ya kuma kara da cewa, a daidai lokacin da kasar ta fuskanci cimma shawo kan cutar, za kuma dole ta tabbatar da ana samar da magunguna da kuma cibiyoyin bayar da shawara ga al’umma don kowa da kowa ya san ana tafiya tare da da shi ba tare da nuna banbanci ba.
Ya kuma ce, za a kara kaimi wajen ganin an isa ga al’ummun da ke wurare masu nisa da wuraren da rikice-rikice ya addaba.
Wani rahoto na musamman da aka fitar a kan ranar kanjamau ta duniya ya nuna cewa duk da namijin kokarin da ake yi na samar da magunguna ga masu fama da cutar da samar magungunan kariya, har yanzu ba a kai ga hawa cikakkiyar hanyar kawo kareshen cutar daga nan zuwa shekarar 2030, babban dalilin haka kuma shi ne rashin daidaiton tattalin arziki dana zamantakewa a tsakanin al’umma.”
Wakilin Nijeriya a hukumar kula da cutar kanjamau ta duniya, wadanda kuma suka shirya gangamin bikin ranar kanjamau ta wannan shekarar 2022, Dakta Leo Zekeng, ya bayyana cewa, “Tabbas muna iya kawo karshen cutar kanjamau, amma ba zamu iya kaiwa ga wannan matakin ba har sai mun kawo karshen matsalolin tattalin arziki da zamantakewa a tsakanin al’umma, ta haka zamu samu cigaban da ake bukata.”
Ya kuma lura da cewa, kawo karshen cutar kanjamau yana nufin samar da issasun kayan gwajin cutar, maganin cutar, hanyaoyin kare cutar musamman ga matasa da wadanda aka bari a baya wajen fara shan magungunan da kuma mutane da rikice-rikice ya tarwartsa a sassan Nijeriya haka kuma da yara kanana masu fama da cutar.
Ya kuma nemi a samar da dokoki na musamman da za su taimaka wajen kawo karshen nuna wariya da banbanci ga al’ummar da suke fama da cutar, ya ce, “Dole a mutunta halin da kowa ke ciki don bashi ya sanya wa kansa ba.”