Rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna ta ce ta kashe ‘yan bindiga 21 tare da kama wasu 780 da ake zargi da aikata laifuka, sannan ta kwato makamai da alburusai 1,408 tare da ceto mutane 206 da aka yi garkuwa da su a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Yekini Ayoku, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a taron manema labarai na shekarar 2022 na rundunar, ya kara da cewa kashe ‘yan bindigar na daga cikin nasarorin da rundunar ta samu a cikin watanni tara da suka gabata.
- Sin Ta Fi Mai Da Hankali Kan Hakikanin Yanayin Yaduwar Cuta Yayin Kandagarkin Annoba
- Gwamnati Na Shirin Karawa Ma’aikata Albashi – Ministan Kwadago
CP Ayoku, ya bayyana cewa 116 daga cikin 780 da aka kama an yanke musu hukunci, yayin da aka kwato dabbobi 1,446 da ak sace su a sassa daban-daban na jihar.
Sai dai ya lissafo nasarorin da rundunar ta samu a cikin wannan lokaci inda ta kama wasu mutane 780 da ake zargi da aikata laifuka da kuma kwato makamai da alburusai 1,408.
Ya kuma mika godiyarsa ga Sufeto-Janar na ‘yansandan Nijeriya Usman Alkali Baba, bisa ganin cancantarsa na ba shi kwamishinan jihar.
Sannan ya yaba wa Gwamna Nasir El-Rufai da sarakunan gargajiya a jihar da kuma jami’an tsaro da kafafen yada labarai bisa goyon bayan da suka ba shi.
A baya-bayan nan dai jami’an tsaro na ci gaba da samun nasara a yaki da suke yi da ‘yan ta’adda a jihar.