A ranar Juma’a ne Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya rantsar da mai martaba sabon Sarkin Jere na 11, Alhaji Abdullahi Daniya a wani gagarumin bikin da aka gudanar a babban filin kwallon kafa na garin Jere.
Bikin wanda ya gudana cikin tsattsauran tsaro, ya samu halartar mataimakiyar gwamnan, Hajiya Hadiza Balarabe da kusan daukacin ‘yan majalisar zartaswa na Jihar Kaduna, da mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, da Jakadan Nijeriya a Kasar Benin, Janar Yusuf Tukur Buratai mai ritaya da Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Isah Jere Idris da sauran manyan baki daga ko ina a sassan kasar nan.
- Zan Fi Mayar Da Hankali Kan Ilimi Da Matasa – Kwankwaso
- NIS Ta Bankado Sabbin Dabarun Da Masu Safarar Mutane Ke Amfani Da Su A Jihar Bayelsa
Da yake jawabi bayan rantsarwar, Gwamna El-Rufai ya jaddada muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’umma wanda ya ce shi ne babban ginshikin kawo ci gaba mai ma’ana. Ya yaba wa al’ummar Jere bisa yadda suka rungumi zaman lafiya tare da yin jaje ga wadanda barnar ‘yan bindiga ta shafa.
Ya kara da cewa, gwamnati na ci gaba da yin duk abin da za ta iya wajen tabbatar da tsaro a fadin Jihar Kaduna, kana ya nemi a kara bai wa jami’an tsaro hadin kai domin su ji dadin dorewa da kwazon da suke nunawa a yanzu haka wajen fatattakar ‘yan ta’addar.
Wakazalika, Gwamna El-Rufai ya yi tsokaci a kan matakan da gwamnatinsa take ci gaba da daukawa wajen kare martabar sarakuna da daga darajojinsu a Jihar Kaduna, inda ya yi nuna da cewa an raba wa Hakimai motoci kuma a yanzu haka gwamnatin na shirin sake raba wasu motoci 88 duk dai ga sarakuna a jihar.
Ya yi kira ga al’ummar Jere su martaba sabon sarkin nasu da ba shi hadin kai don ya ji dadin sauke nauyin da aka dora masa na jama’a. Daga nan ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa Sarkin Jere na 10, Dakta Sa’ad Usman.
Shi ma da yake jawabi, Shugaban Karamar Hukumar Kagarko, Honarabul Auzara Rabo, ya gode wa Gwamna El-Rufai bisa bisa gagarumin ci gaban da ya kawo yankin karamar hukumar da bai wa matasa dama a dama da su a fagen siyasa wanda ya ce hakan ne ya sa aka samu matashi a karon farko da ke shugabantar karamar hukumar.
A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Jere, Alhaji Abdullahi Daniya, ya gode wa dukkan jama’ar da suka halarci bikin, sannan ya jaddada kudirinsa na kara hada kan al’umma da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin masarautar.
Daga bisani, Sarkin Jere ya nada Gwamna El-Rufai sarautar Sarkin Yakin Jere tare da mika masa malafa, da sandar kiwo da kuma katon bajimin sa domin kiwo.