Kamar kowanne mako wannan shafi ya kan zakulo muku fitattun jarumai, har ma da masu tasowa daga cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.
Tare da manyan mawaka har ma da kanana, tana da wadanda suka yi fuce. A yau ma shafin na tafe da bako na musamman wanda ya shafe tsawon shekaru goma a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Jarumi mai taka rawa da kuma shirya fina-finai cikin masana’atar kannywood, kuma shahararren mawakin wakokin Hausa da suka shafi kowanne bangare.
JIBRIN YAHAYA wanda aka fi sani da MISTER D MAIWAKA, Ya bayyanawa masu karatu musabbabin fara wakarsa tare da dalilansa na shiga masana’antar Kannywood, har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’arsa ta fim.
Ga dai tattaunawar tasu tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Ya sunan Malamin?
Sunana Jibrin Yahaya ana kirana da Mister-D Maiwaka.
Me ya sa ake kiranka da Mister-D Maiwaka?
Dalilin da ya sa ake kirana da Mister-D Maiwaka; Inkiya ce wadda lokacin dana fara waka sunan ya canja zuwa Mister D Maiwaka, a baya Dan Alaji ake kira na wannan ‘D’ din ita ce Dan Alaji ta cikin ‘Mister D Maiwaka’. Suna ne na inkiya a takaice kuma sunana ne wanda ko Google mutum yayi ba zai sami irin wannan sunan ba in dai irin yadda nawa yake a rubuce ne.
Masu karatu za su so su ji dan takaitaccen tarihinka?
Mister D Maiwaka an haife ni ne a garin Rimin Zakara, mazabar Rijiyar Zaki karamar hukumar Ungogo Jihar Kano. Na yi firamare a garin Rimin Zakara na kammala sakandare a Rijiyar Zaki 2009, sannan na shiga ‘Amimu Kano College of Islamic and Ligal Studies’, a 2011 na kammala 2013.
Toh! ya batun aiki ko kuma ci gaba da karatu, shin ana yi ko kuwa an ajjiye karatun zuwa wani lokaci?
Tabbas! na ajjiye karatun zuwa wani lokaci, sakamakon Allah ya yi min fikira ta bangare biyu, ina harkar wayarin na gida da kuma waka, wannan sana’o’in su suka sa na ajjiye karatu, amma ina san komawa karatu. Batun aiki kuma gaskiya ni ban taba ‘apply’ na aikin ‘gobernment’ ba.
Wanne irin rawa kake takawa a cikin masana’antar kannywood?
Ina Furodusin na fim kuma sannan na yi Aktin.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma harkar waka?
Tun farkon shigowata kannywood, gaskiya ba abun da zan cewa Allah sai godiya, Saboda ban taba waka ba na je har gidan dan majalisa na Ungogo wato Faruk Mohd Bachirawa, bayan mun gaisa na gabatar da kaina na ce zan masa waka nan take ya yi ‘accept’ ya rubutan sunaye ya dauki kudi ya ban, na je na yi na kawo masa, karshe dai sai da ya kasance ni ne mawakinsa, ko waye zai masa waka a wannan lokacin sai ya ce wakata ya ke so. Kaninsa ma ya sa wani ya yi ya ce masa ina! take ya ba shi nambata ya ce ya kira ni ni zan yi domin muryata ya ke so. A kwana a tashi na tsinci kaina cikin wakar nadin sarauta ta Balarabe Abba Iliyasu dagachin Rimin Zakara, daga nan sai wakokin biki suka runka zuwar min har ta kai ga ba wata waka da bana yi a yanzu, yau gani na tsinci kaina a cikin
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Alhamdulillah na shiga kannywood domin na taimaka wa na kasa da ni, sakamakon suna bukatar shiga ciki ba su da hanya, kuma na dauki harkar sana’a da kuma lissafin tura sako ta fuskar farantawa ‘yan uwa abokan arziki. Kuma da fadakar da su abun da ba su sani ba, da kuma abun da suka manta.
A wanne fim ka fara fitowa?
‘Goyan Kaka’ na taka rawa inda na fito a saurayi na je zance wurin budurwa, sannan akwai wani kuturu wanda yake sonta na je zance ya zo zance, nan ya hau yi mata fada karshe ba ta ce komai ba, ya dawo kaina da ‘proud’ na cewa shi mai kudi ne dan haka zai siye ni, inda nake ce masa ina kudin ya nuna, ‘yan tsirarin kudi. Nan take na kada shi ta fuskar; Da shi da komai nasa ni zan saye su in aka yi min gwanjensu domin ni kudina na ‘bank’ ne, akwai Gwanja, akwai Bosho.
Za ka yi kamar shekara nawa a cikin masana’antar kannywood?
A Kalla zan yi kamar shekara goma 10 cikin masana’antar.
Ko za ka iya fadawa masu karatu yawan adadin fina-finanka?
Gaskiya ba zan iya musalta adadin fina-finan da nayi ba, domin wani lokacin a rana daya sai kayi aiki kusan uku, wannan ne ya sa tun ina kirgawa har na daina.
Ko za ka fada wa masu karatu kadan daga sunayen fina-finan da ka fito ciki?
‘GOYON KAKA na su Ado Gwanja, SAKIN FUSKA na Suleiman Super Star, SHARRIN ZUCIYA da kuma NA RAMMA, na Salisu Mu’azu, sai nawa dana fito a ciki mai suna DAN DAKO, da kuma ZURFIN CIKI, akwai kuma fim din KUJERAR TSAKAR GIDA, na Raji Abdallah wanda Ado Gwanja yayi Furodusin.
Da wanne Jarumi da Jaruma ka fara fitowa a fim?
Jurumin dana fara aiki da shi Ado Gwanja da Bilkisu M. Ahmad.
Nawa ne adadin wakokin da ka yi, kuma wacce ce ta fi yin fuce?
A kalla ina da wakoki na soyayya za su yi dari biyu idan an hada da wakokin biki, suna, da birthday, siyasa, za su yi kimanin dari uku.
Da wacce Jaruma ka fi yin waka?
Jarumar dana fi yin waka da ita, ita ce; Jaruma Rukayya M. Inuwa.
Me kake son cimma game da fim da kuma waka?
Ina bukatar yau ace gani na zama tauraro, domin taimakawa na kasa da ni ‘yan uwa da abokan arziki da addini na.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin hakan game da fim ko waka wanda ba za ka manta da shi ba?
Lokacin dana ke daukar wata wakata mai suna ‘Kaddarar So’, gaskiya wannan lokacin ina cikin farin ciki amma da marigayi Abdulwahab Awarwasa yana dukana sai na ji kamar gaske ne, jarumar matar sojan ce.
Wanne irin Nasarori ka samu game fim da kuma waka?
Gaskiya na sami nasarori sosai, domin nakan sami ayyuka da wokokin biki, da kuma fina-finai sosai. Dan kafin yanzu haka ina tare da Director Salisu Mu’azu R/zaki muna aiki, bayan ya kira ni wayar na caji bai samu shigar kiran ba, sai turo abokina da ya yi har gida ya zo ya gayan cewa Director yana jirana za mu yi aiki, wanda a ‘studio’ ana jirana amma na ba su hakuri cewa sai dare zan zo ‘studio’ ina wani aiki.
Toh! Ya batun kalubale fa?
Gaskiya ban fuskanci wani kalubale ba, domin ni abun da ban yadda da shi ba tun ina yaro ka zo ka ce wane ya ce min kaza, haka ne ya sa ni kowa rayuwa mai dadi nake da shi, in ma kai kana nufina da wata manufa ba abun da ya shamin kai, domin Allah nasa a gaba, kuma na tabbata zai hisabi akan hakkina.
Lokacin da za ka fara harkar fim shin ka fuskanci wani kalubale daga gida yayin da ka sanar wa iyayenka?
Gaskiya ban fuskanci kalubale ba, domin mahaifina daga ran da na ce zan fara ya samin albarka, haka mahaifiyata kalmar bakinta “ka kula da rayuwarka a duk inda kake”.
Mene ne burinka na gaba game da fim da kuma waka?
Burina yau ace na zama tauraro idan na tura sako zai je ko ina cikin yardar ubangiji da gaggawa, na san zan bawa mutane gudunmowa ta alkhairi.
Za mu ci gaba mako me zuwa in sha Allah.