Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a dakatar da ma’aikata guda 3,000 bisa zarginsu da yin amfani da takardun bogi wajen daukar su aiki a ma’aikatun gwamnatin Tarayya.Â
Shugabar ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Dakta Folasade Yemi-Esan ce ta sanar da hakan a Abuja a lokacin da take tattaunawa da manema labarai a Abuja yayin da da ake shirye-shiryen gudanar da bikin murnar ranar ma’aikata ta shekarar 2022.
Yemi-Esan ta ci gaba da cewa, an bankado sunayen ma’aikatan ne a yayin ci gaba da tantance ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
Ta kara da cewa, wannan sabon bankado sunayen an yi ne bayan an gano wasu sunayen ma’aikatan 1,500 wadanda suka gabatar da takardun bogi a watan Afrilun 2022.
A karshe, Yemi-Esan ta bayyana cewa, in ba a manta ba a baya, sama da ma’aikata 1,000 ne a baya a ma’aikatar yada labarai aka bankado sun gabatar da takardun bogi wajen daukar su aiki, inda kuma aka sake gano guda 500 a wasu ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da a wasu sassa da hukumomi 500 na Gwamnatin Tarayya.