Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya ce dazarar ya kammala wa’adin mulkinsa wa’adi na biyu zai yi ritaya a siyasa.
Gwamnan ya sanar da haka ne a lokacin da yake karban bakwancin mambobin kungiyar mai zaman kansa wato, ‘Correspondents Chapel’ na kasa reshin Jihar Nasarawa wadanda suka kai masa ziyarar taya shi murnar bikin karamar Sallah da aka gudanar a gidansa da ke garin Gudi a yankin karamar hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa.
- Kayayyakin Da Aka Shige Da Fice Na Ayyukan Yawon Shakatawa Na Sin Sun Karu A Cikin Rubu’i Na Farko A Bana
- Yan Bindiga Sun Sace Masu Ibada 40 A Coci, 15 Sun Kubuta A Kaduna
Ya ce a yanzu ya cimma burin rayuwarsa na kasancewa gwamnan Jihar Nasarawa. inda ya samu damar ba da nasa gagarumin gudumawa wajen ci gaba jihar a dukkan matakan rayuwa.
A cewar gwamna Sule, zuwan sa kan karagar mulkin jihar ke da wuya sai ya tarar da dinbin kalubalai, amma nan da nan sai ya yanke shawarar yin duk mai yuwa wajen tabbatar jihar ta cimma takwarorin ta, musamman a fannin kasance daya daga cikin jihohi da suka bunkasa a fannin ma’adanai. Ya ce a yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu, domin ya cimma burinsa na rayuwa.
Ya ce, “Ina so in yi amfani da wannan dama na sanar da ku cewa ba ni ba sake fitowa takarar kowanna kujerar siyasa a jihar nan bayan na kammala wa’adina mulkina karo na biyu a matsayin gwamnan Jihar Nasarawa.
“Kuma na yanke shawarar ne don a yanzu kamar yadda kuka sani na cimma burina na ba da gagarumin gudumawa wajen ci gaban jihar nan a dukkan matakai, musamman a fannin ma’adanai da albarkatun kasa da sauran su.
“Jihar ta yi daidai da sauran jihohin kasar nan sabanin yadda lamarin yake a baya kafin in zama gwamna,” in ji shi.