Shugaba cocin nan na Kenya da ake zargi da laifin tilasta wa mabiyansa azumin mutuwa don haduwa da Yesu Almasihu ya sake bayyana a gaban kotu ranar Larabar nan, bayan gurfana da ya yi a ranar Talata.
Hukumomi na gudanar da bincike kan yiwuwar cewa an yi amfani da sassan jikin mutanen da suka mutun.
- Zaɓen Gwamna: INEC Ta Fitar Da Sunayen ‘Yan Takarar Zaɓuɓɓukan Cike Gurbi Na Jihohin Kogi, Bayelsa Da Imo
- Majalisa Ta 10: Zababbun Sanatocin APC Na Arewa Ta Tsakiya Sun Yi Fatali Da Zabin APC
Binciken ‘yan sanda ya nuna yadda aka gano karin wasu gawawwakin da aka cire sassan jikinsu.
Wannan ya sa ake ganin da alama an yi amfani da sassan jikin gawawwakin mabiyan na Cocin Good News International, da aka gano a dajin Shakahola na kasar ta Kenya.
Kusan a kullum aka ci gaba da binciken da ake yi tun da aka fara gano wannan al’amari a tsakiyar watan Afrilu sai an samu karin gawawwaki, inda yanzu aka samu 133.
Ana zargin shugaban cocin Good News International, Pastor Paul Mackenzie mai shekara 50 da sanya mabiyansa azumi har su mutu, ko su kashe kansu a dalilin hudubar da ya yi musu cewa duniya za ta tashi ranar 15 ga watan Afirilun da ya gabata.
Ya gaya musu cewa idan suka mutu za su shiga aljanna inda za su hadu da Yesu Almasihu.
Mutanen da aka gano sun mutu ko dai a dalilin azumin da ya kai su ga yunwa har suka mutu ko kuma an shake su ko kuma sun mutu a dalilin buga musu wani abu.
Kungiyar agaji ta Red Cross a kasar ta Kenya ta ce har yanzu akwai mutane 566 da ba a san inda suke ba.
Yayin da mai binciken gawawwaki na gwamnatin kasar ya ce ko dai gawawwakin sarai suke ba a cire wani sashe na jikinsu ba, ko kuma wasu sassan nasu sun fara rubewa, binciken ‘yan sanda ya nuna sabanin hakan.
An gano cewa an ciccire sassan jikin wasu, wanda hakan ke nuna yuwuwar an yi amfani da sassan jikin mutanen.
Ministan tsaro na Kenya ya ce wannan lamari wani mugun laifi ne da aka tsar shi sosai, kuma aikin tono gawawwakin zai dauki lokaci fiye da yadda aka yi tsammani.
A halin da ake ciki kuma an rantsar da wata hukumar bincike ta musamman a babban birnin kasar Nairobi, da kuma wani kwamiti na musamman da na sanya ido a kan harkokin addini domin su gudanar da bincike a kan lamarin.
Masu binciken laifuka a Kenya sun tono karin gawarwaki 21 bayan kaddamar da sabon bincike kan lamarin.
Ministan cikin gida na Kenya Kithure Kindiki ya ce su na binciken ko an yanke gabobin wasu gawawwakin don safarar gabobi.
An dakatar da tono gawawwakin saboda rashin kyawun yanayi a dajin na Shakahola.
An fara tuhumar faston tare da wasu mutanen 14 kan laifukan ta’addanci da dora mutane kan tsattsaurar akida.