Tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya kuma dan takarar Sanatan Bauchi ta Arewa a karkashin jam’iyar Social Democratic Party (SDP) a zaben 2023, Hon. Ibrahim Mohammed Baba IMBA ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
IMBA wanda ya shelanta komawa jam’iyyar a ranar Juma’a kuma ya samu tarba daga wajen shugaban jam’iyyar APC a gundumar Nasarawa Bakin Kasuwa a karamar hukumar Katagum, Adamu Abubakar da suka karbe shi a ofishin jam’iyyar da ke gundumar.
- Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 8, Ya Jikkata 7 A Bauchi
- Gwamnan Bauchi Ya Nada Sarkin Ningi A Matsayin Amirul Hajj Na 2023
IMBA ya kasance dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Katagum tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 da ya samu nasarar tafiya majalisar a karkashin jam’iyyar APC daga bisani kuma ya fice daga jam’iyyar bayan wasu ‘yan matsaloli.
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida kan dalilinsa na sake dawowa cikin jam’iyyar APC, Ibrahim Baba IMBA ya ce sun dawo tare da magoya bayansa ne domin gina jam’iyyar da sake farfado da ita, kana ya na mai cewa dukkanin matakan da suka dace na gyara jam’iyyar za su yi.
Ya ce, “Babban dalilina shi ne muna son mu dawo mu sake gina ita jam’iyyar saboda ta dawo hayyacinta. Kamar a 2015 an fusata mutane da yawa, mutane sun yi fushi sosai a jihar Bauchi saboda wasu dalilai, hakan ya sanya wadansunmu suka fita, wasu sun dawo wasu kuma har yanzu ba su dawo ba, wasu kuma har yanzu din su na cikin jam’iyyar amma ba su taimakonta.
“Wannan dalilin ya sanya muka ce bar mu dawo domin a zo a gyara tsarin.”
Ya ce su na sane har yanzu har gobe hankalin al’ummar jihar Bauchi na kan jam’iyyar APC, “Dawowarmu din zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da ake fama da su musamman rikicin cikin gidan nan. Idan muka samu zo muka zauna muka samu wadanda lamarin ya shafa tun da mu din ma mun fita amma mun san ciwon da ya sa muka fita, don haka da yardar Allah za mu samu masu ruwa da tsaki a zo a ga an zauna da su domin tabbatar jam’iyyar ta sake samun nasara a gaba kuma al’umma su mori nasarar da aka samu.”
A cewarsa, babu abun da tattaunawa ba zai gyara shi ba, don haka ya ce rikicin cikin gida da ke APC za su yi kokarin magance shi nan ba da jimawa ba, “Duk lokacin da mutane suka zauna suka fitar da abubuwan da suke ganin ya dace a yi da wadanda suke ganin bai dace a yi ba, ta haka za a samu mafita kan matsaloli sosai.”
IMBA ya kuma shaida cewar sai da ya tuntubi magoya bayansa da masu ruwa da tsaki kafin daukan wannan matakin inda suka mara masa baya tare da sake biyo shi suka dawo APC.
“Na tuntubi magoya bayana sosai kafin muka dauki wannan matakin, kuma tun lokacin da muka koma ita wancan jam’iyyar har muka yi takara magoya bayana da dama basu fito sun shiga wancan jam’iyyar ba, sun dai je sun mara mana baya ne a zabe wanda kowa ya ga yadda zaben ya kasance musamman a karamar hukumata ta Katagum, wannan dalilin ya sanya dole mu sauraresu mu dawo mu kula da wadanda suka fi bukatar mu yi mu’alamar siyasa da su.”
Shi ma a nasa bangaren, shugaban jam’iyyar APC a gundumar Nasarawa Bakin Kasuwa a karamar hukumar Katagum, Adamu Abubakar, ya nuna jin dadinsu bisa dawowar IMBA cikin jam’iyyar, yana mai cewa tabbas jam’iyyar cike take da farin cikin samun irinsa lura da irin tasirin da ke da shi a siyasance.
Ya kuma bada tabbacin cewa a matsayinsa na mai fada a ji, zai kawo cigaba musamman wajen tabbatar da hadin kai da cigaban jam’iyyar, sai ya masa lale da dawowa jam’iyyarsa ta asali.