Biyo bayan dakatar da aikin jigilar matafiya a jirgin kasa da hukumar jiragen kasa ta Nijeriya ta yi a kwanan baya, hukumar ta sake dawo da jigilar matafiya daga Abuja zuwa Kaduna.
A ranar Lahadi aka dawo da jigilar fasinjojin Jirgin daga tasharsa da ke a Idu a Abuja, ya tashi da misalin karfe 9.45 na safiyar ranar Lahadi, haka kuma wani Jirgin ya taso zuwa tasharsa ta Rigasa da ke a Kaduna da misalin karfe 1.30 na ranar Lahadi.
- Bukatar Magance Yawaitar Hatsarin Jirgin Kasa A Nijeriya
- Sama Da 280 Ne Suka Mutu, 1000 Suka Jikkata A Hatsarin Jirgin Kasa A Indiya
Wata sanarwa da Leadership ta samu ta nuna yadda Jirgin ya taso daga Kaduna zuwa tasharsa ta idu da ke Abuja da misalin karfe 3.00.
A cewar sanarwar daga ranar Litinin 5 ga watan Yunin 2023 Jirgin ya tashi zuwa tashar Rigasa da misalin karfe 8.00 na safe, inda kuma wani Jirgin ya tashi daga Idu, da misalin karfe 9.45 na safe.