Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada umarnin kai samame gidan tsohon gwamnan jihar, Muhammad Bello Matawalle tare da kwace wasu motoci da ake kyautata zaton na gwamnatin jihar ne.
A ranar Juma’a ne aka kwace wasu motocin a gidan Matawalle da ke Gusau.
- Motocin Fasinja Kirar Sin Da Aka Sayar Sun Karu Da Kashi 37.6 A Mayu
- Sabon Shugaban Kamfanin Jiragen Saman Nijeriya Ya Yi Tonon Silili
Idan za a iya tunawa, da yake magana a wani gidan rediyon yankin, Gwamna mai ci Dauda Lawal ya ce, “Tsohon Gwamna Bello Matawalle ya tafi da motoci 17 daga ofishinsa da kuma wadanda ke ofishin mataimakin gwamna yana mai cewa motocinsa ne, asali ma kayan ofis ma ba su tsira ba.”
A cewar wani rahoto, an kwashe motoci kirar jeeps masu sulke guda hudu.
An ce ‘yansanda sun kai farmaki gidan tsohon gwamnan, wanda ba shi da nisa da gidan gwamnati a Gusau, babban birnin jihar.
LEADERSHIP ta rawaito cewa Gwamna Lawal ya zargi Matawalle da yin awon gaba da motocin gwamnati tare da wawashe kadarori da suka hada da talabijin da kayan dafa abinci a gidan gwamnatin jihar da ofishin hulda da jama’a na jihar da ke Abuja.
A ranar Asabar din da ta gabata ne, Lawal ya bai wa Matawalle wa’adin kwanaki biyar ya mayar da motocin da ake zargin jami’an gwamnatinsa sun tafi da su.
Lawal wanda ya bada wa’adin ta wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Idris ya fitar, ya sha alwashin kwato kudade da kadarorin gwamnatin jihar da aka sace.
“Muna da hujjoji da bayanan da ke nuna rashin dacewar Matawalle. Ina karyar ta ke? Tsohon gwamnan ya bayar da kwangilar sayen motocin da za a raba wa manyan ma’aikatu kan kudi Naira biliyan 1,149,800,000.
“An bayar da kwangilar siyan motocin ga kamfanin Hafkhad Properties and Facilities Management Nig. Ltd.
“An yi amfani da kudin ne don siyan mota kirar Toyota Lexus VIP mai kare harsashi.
“Mun sanar da tsohon Gwamna Bello Matawalle da Mataimakinsa a hukumance cewa su dawo da dukkan motocin da suka bace cikin kwanaki biyar,” in ji shi.
A lokacin da LEADERSHIP ta tuntubi gwamnatin Jihar Zamfara kan lamarin, mai magana da yawun Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya shaida wa wakilinmu cewa bai da masaniyar cewa shugaban nasa ne ya bayar da umarnin kai samamen, inda ya ce ‘yansanda na yin aikinsu ne kawai.