Gwamnatin Jihar Kogi ta fara gudanar da bincike a kan wasu manyan sarakunan Jihar guda biyu game da wani mummunan tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane tara tare da kone gidaje da dama a karamar hukumar Bassa da ke jihar.
Rahotanni dai sun nuna cewa manyan sarakunan guda biyu, masu daraja ta daya sun hada da Alh. Khalid Ali Bukar Sarkin Mozum, Sarkin Bassa da kuma Chif William Keke dukansu a yanzu haka suna hannun hukumomi a jihar domin gudanar da bincike a kan lamarin.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace DPO A Kaduna
- G7 Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Taimakon Ukraine A Yakinta Da Rasha
Gwamnatin jihar dai ta ce yankin na Bassa ya dade yana fama da tashin hankali da ya shafi kabilanci da kuma rikicin mallakar filaye a tsakanin ‘yan kabilar Egbira da kuma Bassa Komo.
Al’amarin da gwamnatin jihar ke gani sarakunan na da rawar takawa wajen shawo kan wannan matsala kamar yadda kwamishinan labarai na jihar Kogin Mr. Kinsley Fanwo, ya yi karin bayani, inda ya ce ba wai an kama su bane, an gayyace su ne domin su yi karin haske a kan matsaloli da dama da za su taimaka wajen dorewar zaman lafiya a wannan karamar hukuma ta Bassa.
Fanwo, ya ce gwamnati ta yi kokarin dawo da zaman lafiya a yankin, kuma akwai wani tsari da aka samar da zai hana aukuwar abin da ya faru a baya.
Daya daga cikin sarakunan yankin da aka kone gidansa sakamakon tashin hankalin, yanzu haka ya ke gudun hijira, wato Hakimin Mozum, Alh. Haruna Abubakar, ya ce duk da suna gudun hijira, a yanzu haka suna kokarin karbar Belin Babban sarkin nasu.
Masu sharhi a kan lamurran tsaro dai na ganin matakin rike manyan sarakunan yankin, watakila ya taimaka wajen gano bakin zaren da zai taimaka wajen shawo kan matsalar tashin-tashina da a aka dade ana fama da ita a yankin.