Masu zanga-zanga a kasar Kenya sun yi ta jifa da duwatsu kan ‘yansanda, wadanda suka mayar da martani da barkonon-tsohuwa, a wani artabu da aka yi a manyan biranen kasar.
An kwashe kwanaki uku ana zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa da karin haraji a kasar da ke gabashin Afirka.
- Babu Sulhu Tsakaninmu Da ‘Yan Fashin Daji -Gwamnatin Zamfara
- Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Sayar Da Hannun Jarin Wasu Tashoshin Jiragen Sama
Motoci biyu masu dauke da ruwan zafi da ‘yansandan kwantar da tarzoma da dama ne aka jibge a kofar shiga unguwar Kibera a birnin Nairobi.
Inda masu zanga-zangar suka kona tayoyi tare da fafatawa da jami’an tsaro.
Har yanzu dai babu cikakken bayani kama daga bangaren gwamnati ko kuma ‘yan adawa.
An rufe makarantu a Nairobi babban birnin kasar, da kuma birnin Mombasa mai tashar jiragen ruwa hadi da Kisumu, birni na uku mafi girma a kasar.
Akalla mutane 15 ne aka kashe tare da kame daruruwa a zanga-zangar da aka yi a farkon wannan watan, lokacin da ‘yansanda suka harba barkonon tsohuwa kan dandazon jama’a.