Wani jirgi mai saukar ungulu na dakarun mayakan sojan saman Nijeriya (NAF) ya gamu da hatsari a kauyen Chukuba da ke cikin karamar hukumar Shiroro a jihar Neja a ranar Litinin.
Jirgin wanda ya yi hatsarin a hanyarsa ta zuwa Kaduna daga jihar Neja yayin da ke sintirin kwaso wadanda aka jikkata.
- Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Neja Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa
- Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Sai dai babu wani bayanin da ke nuna akwai wadanda suka jikkata ko kuma wadanda suka tsira a hatsarin a zuwa lokacin hada wannan rahoton yayin da NAF ta ce ta na kan kokarin ceto wadanda suke cikin jirgin a lokacin da ta yi hatsari.
A cewar jami’in watsa labarai na rundunar sojin saman Nijeriya, Air Cdre Edward Gabkwet, ya ce a wata sanarwa, jirgin ya gamu da hatsarin a lokacin da ke aiki kwaso wadanda suka jikkata kafin ya yi hatsarin wajajen karfe 1 na rana.
Sanarwar ta ce, “Jirgin NAF mai lamba MI-171 Helicopter da ke aikin kwaso wadanda aka jikkata ya gamu da hatsari a yau, a daidai kauyen Chukuba da ke jihar Neja. Jirgin ya tashi ne daga makarantar firamare na Zungeru zuwa Kaduna sai daga baya aka gano ya gamu da hatsari a kusa da kauyen Chukuba Village a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
“Yanzu haka ana ta kokarin ceto matuka jirgin da fasinjojin da ke cikin jirgin, yayin da aka kaddamar da bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin.”