Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce, adadin wadanda suka yi rijista su 1,955,657 ne za su samu damar jefa kuri’a a zaben gwamnan Jihar Osun da zai gudana a ranar 16 ga watan Yuli na 2022.
Babban kwamishinan INEC kuma Shugaban sashen yada labarai da ilmantarwa, Mista Festus Okoye, shine ya shaida hakan a wajen tattaunawa da shugabannin kafafen yaɗa labarai a ranar Juma’a a Osogbo.
- INEC Ta Nuna Damuwa Kan Karancin Masu Fitowa Karbar Katin Zabe A Katsina
- 2023: INEC Ta Kara Wa’adin Ranakun Yin Katin Zabe
Okoye ya kara da cewa, jam’iyyun siyasa 15 ne za su shiga a dama da su a zaben da ya kunshi kananan hukumomin 30 na jihar.
Sannan, ya bukaci shugabannin kafafen watsa labarai a jihar da su tabbatar da an gudanar da sahihin zabe mai cike da gaskiya da adalci.
Kazalika, hukumar ta kuma yi gargadi dangane da masu yin katin rijistan jefa kuri’a ‘Permanent Voter Cards’ (PVC) fiye da guda daya da cewa lallai za su fuskanci fushin hukumar tare da barazanar gurfanar da duk wanda aka kama da hakan.
Kwamishinan hukumar INEC a jihar Oyo, Mutiu Agboke shine ya yi gargadin a jiya a Ibadan yana mai cewa, hukumar ta samar da wasu karin mashina domin tabbatar da aikin katin PVC ya cigaba da gudana cikin nasara.
Ya ce, samar da karin mashinan an yi ne domin tabbatar da duk wanda ya cancanci jefa kuri’ar ya samu damar yin hakan.