Jam’iyyar PDP reshen jihar Osun ta bai wa Kwamishinan Rundunar ‘yan sanda na jihar Olawale Olokode wa’adin sa’o’i 24 na yiwa wa alummar jihar bayani kan dalilin da ya sa wasu Jami’ansa ke yi wa ‘ya’yan PDP a jihar dauki dai-dai.
Wannan wa’adin na kunshe ne a cikin sanarwar da shugaban kwamitin riko na PDP a jihar Akindele Adekunle ya fitar inda ya ce, Jam’iyyar na bukatar bayanai daga gun Kwamishinan kan yadda ake ci gaba da yiwa ‘ya’yanta da ke a jihar dauki dai-dai.
Akindele ya kuma zargi Kwamishinan ma’aikarar ayyuka da sufuri na jihar Remi Omowaye kan zarginsa da yin amfani da wasu ‘yan sanda a jihar wajen zuwa gidajen ‘ya’yan PDP a jihar da ke a wasu kannan hukumomi a jihar domin kama su.
Ya yi zargin cewa, wasu Jami’an ‘yan sanda a jihar, sun dira ne a gidajen wasu ‘ya’yan PDP da tsakar dare a yankunan Ijebu-Ijesa da Eti Oni a kananan hukumomin Oriade da Atakumosa ta gabas, inda suka yi awon gaba da su.
Shugaban ya kuma zargi jami’an tsaro na sa kai na Amotekun kan hantarar wasu al’ummar jihar, inda ya yi nuni da cewa hakan ya saba manufar kirkiro da Jami’an da Gwamnatin jihar ta yi.