Ana ci gaba da tafka muhawara dangane da yawan makarraban da wasu gwamnoni suka nada a jihohinsu.
Mutane da dama musamman ma ‘yan adawa na sukar lamarin, sakamakon koma bayan da ake samu na raguwar tattalin arziki bai kamata a kara yawan tsadar gudanar da harkokon gwamnati ba, wanda suka yi kira da gwamnoni da su kara yin nazari.
Jerin jihohin da lamarin ya shafa sun hada da Adamawa, Neja, Kano, Akwa Ibom, Filato da kuma Ebonyi.
Jihar Adamawa
A Jihar Adamawa, gwamna Ahmadu Umaru Fitiri ya yada makarrabai masu ba shi shawara kan harkokin yada labarai har guda 46, inda masu ruwa da tsaki da dama ke ganin hakan a matsayin almubazzaranci.
Babban sakataren yada labarai na gwamnan, Humwashi Wonosikou shi ya fitar da sanarwar nadin mukarraban har guda 46.
Mukarraban sun kunshi mashawarta na musamman guda biyu, manyan mataimaka na musamman guda 10 da mataimakan kafofin yada labarai har guda 34.
“Gwamna Fintiri ya amince da nadin mashawarta na musamman guda biyu, manyan mataimaka na musamman da mataimaka na musamman da za su yi aiki a matsayin masu taimakan gwamnan kan harkokin yada labarai. Masu ba da shawara na musamman guda biyu su ne, Dakta John Ngamsa (sadarwa da dabarun) da Babayola Toungo (yada labarai da hulda da ‘yan jarida).
“Nadin da ya fara aiki nan take sun hada da George Kushi, babban mai bayar da shawara kan harkokin yada labarai da hulda da ‘yan jarida, Ijafiya Domiya, mashawarci kan yada labarai na zamani, Sherif Alhassan, mai bayar da shawara kan harkokin yada labarai na intanet, Muhammed Tukur, mai bayar da shawara kan sabbin harkokin yada labarai, Nurudeen Kama, mai bayar da shawara kan sabbin hanyoyin sadarwa, Pius Iliya, mai bayar da shawara kan sabbin hanyoyin sadarwa, Auwal Hamza, mai bayar da shawara kan sabbin hanyoyin sadarwa, Thomas Terry, mai bayar da shawara kan harkokin daukan hoto, Sunday Wugirah, mai bayar da shawara kan harkokin jama’a da Bictor Dogo, mai bayar da shawara kan harkokin hada kan jama’a, yayin da sauran 34 aka hada su a matsayin mashawarta na musamman kan harkokin yada labarai,” in ji sanarwar.
Bayan watanni biyu, a ranar 6 ga Oktoba, mai magana da yawun gwamnan ya fitar da wani jerin sunayen mataimaka 103 da suka hada da manyan jami’ai na musamman 37, manyan mataimaka na musamman 45 da wasu mataimaka na musamman 21.
Mukarraban Guda 149 Za Su Lakume Naira Miliyan 28 Duk Wata A Adamawa
Majiyoyi sun bayyana cewa albashin manyan mataimaka na musamman a kowane wata ya haura naira 300,000, yayin da manyan jami’ai na musamman da mataimaka na musamman ke karbar naira 240,000 da naira 180,000 a duk wata.
Hakan na nuni da cewa za a kashe sama da naira miliyan 28 don kula da mataimakan siyasa da gwamnan ya nada.
Sai dai sakataren yada labaran gwamnan ya ki amincewa da cewa adadin ya yi yawa kuma ba almubazzaranci ba ne daukan mataimakan domin yin farfagandar siyasa wajen kai wa abokan hamayya harin baka.
A cewarsa, an bai wa kowane daya daga cikin wadanda aka nada akinsa. Ya ce nadin zai kuma zama wani mataki na rage radadin talauci a jihar.
Jihar Neja
A Jihar Neja, nadin mukarrabai da gwamna Mohammed Umaru Bago ya yi ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan kasar ciki har da wasu jami’an jam’iyyar APC na jihar.
A kwanan nan ne gwamnan ya ba da mukamai ga sabbin jami’ai mata guda 41 da aka nada mukamai daban-daban da suka hada da ko’odinetocin harkokin siyasa da harkokin yada labarai da hulda da jama’a da kula da lafiyar mata da kananan yara da lauyan gidan gwamnati da kungiyar tallafa wa mata da horar da mata.
Bugu da kari, an bai wa mata manyan mataimaka na musamman guda 90 mukaman siyasa da dai sauransu.
Wasu daga cikin mazauna jihar sun bayyana cewa kudaden da za a kashe kan wadannan makarrabai zai isa a gyara muhimman bangarorin gwamnati, musamman fannin lafiya da ilimi.
Wani jigon APC da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana cewa mafi yawancin matan da gwamna ya nada su 131 ba su janjanta ba. Ya kara da cewa nadin zai kara tsadar harkokin gudanarwar gwamnati.
Za A Kashe Wa Makarraban 131 Naira Miliyan 23.7 Duk Wata A Neja
Duk da cewa sabbin manyan mataimaka na musamman da ko’odinetocin da aka nada an ce ba a ba su takardun fara aiki ballantana su karbi albashi, amma majiya mai tushe ta shaida cewa albashin babban mataimaki na musamman bai kasa naira 150,000 ba bayan an cire haraji, yayin da ko’odinetocin ba za su gaza amsar albashi na naira 250,000 ba.
Masu ba da shawara na musamman wadanda aka bayyana cewa albashinsu ya yi daidai da na kwamishinoni, za su karbi albashin da bai gaza naira 350,000 ba, yayin da aka ce albashin mataimaka na musamman ba zai gaza naira 120,000 ba.
An gano cewa gwamnatin Jihar Neja za ta kashe naira miliyan 10,250,000 wajen biyan albashin kodinetoci mata 41 da kuma naira miliyan 13,500,000 duk wata don biyan albashin manyan mataimaka na musamman 90 da aka nada.
A dunkule dai, za a kashe akalla naira miliyan 23.7 domin kula da mataimakan mata 131, baya ga albashin sauran wadanda aka nada.
Majiyoyi sun ce akalla za a kashe naira 10,500,000 duk wata don biyan albashin masu ba da shawara na musamman guda 30.
Sai dai babbar sakatariyar yada labaran gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce nadin da aka yi wa mata 131 a matsayin kodinetoci da manyan mataimaka na musamman ya kasance cika alkawarin da gwamnan ya yi wa mata a lokacin yakin neman zaben gwamnan na bai wa mata mukamai masu gwabi a gwamnatinsa.
Jihar Kano
A Jihar Kano, gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada mataimaka 406 da ke yi masa aiki.
Wannan baya ga kwamishinoni, daraktocin ma’aikatu da rassan gwamnati da hukumomi da sauran wadanda aka nada.
Daga cikin wadanda aka nada akwai mataimaka na musamman, masu ba da shawara na musamman, manyan jami’a na na musamman da kuma manyan jami’ai masu bayar da rahotanni na musamman.
Yayin da nada mataimaka na musamman da masu ba da shawara na musamman da manyan jami’ai na musamman sun kasance ruwan dare ga kowace gwamnati, manyan jami’ai masu bayar da rahotanni na musamman su ne sababbi a gwamnatin Jihar Kano.
Babban sakataren yada labarai na gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce nadin ya zo ne domin cika alkawarin da gwamnan ya yi na gudanar da harkokin gwamnati mai gaskiya da za ta tafiyar da al’umma.
Ya ce nadin wani mataki ne na cika manufar gwamnatinsa na samar da ayyukan yi, shigar da matasa harkokin mulki da sauya hanyoyin samun bayanai.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye, ya ce idan aka yi la’akari da yawan al’ummar jihar, mataimakan ba su ma isa ba.
Ya ce gwamnatin jihar na yin hakan ne domin tabbatar da cewa gwamnati ta kasance cikin gaskiya da kuma kusanci ga jama’a.
Mukarrabai 251 Za Su Lakume Naira Miliyan 36.6 A Duk Wata A Kano
Binciken ya nuna cewa sabbin mataimakan ba su da masaniyar adadin albashin da za a biya su, saboda takardar nadin nasu ba ta kunshi tsarin albashin su ba.
Sai dai kuma an tattaro cewa gwamnatin da ta shude ta biya wasu manyan mataimaka na musamman naira 70,000 a matsayin albashi tare da karin sama da naira 50,000, wanda ya kai na naira 120,000 a duk wata daya.
An ce gwamnatin da ta shude ta biya masu ba da shawara na musamman albashin naira 200,000.
Idan har gwamnati mai ci za ta ci gaba da biyan su haka za ta biya naira miliyan 20,280,000 a cikin wata guda, domin biyan albashin mashawarta na musamman 169 da gwamnan ya nada.
Haka kuma gwamnatin za ta kashe zunzurutun kudade na naira miliyan 16, 400,000, wajen biyan albashin mataimaka na musamman guda 82 da gwamnan ya nada.
Har yanzu dai ba a tantance albashin manyan jami’a masu bayar da rahoto guda 138 ba da aka tura ma’aikatu da hukumomi, saboda sabon tsarin ne. Sai dai akwai rahotannin da ke cewa za a biya su alawus-alawus daga hukumomi daban-daban da suke ba da rahoto.
Jihar Akwa Ibom
A Jihar Akwa Ibom, gwamna Umo Bassey Eno ya rantsar da wasu mataimaka 368 da aka zabo daga kowace shiyya a fadin jihar, domin taimaka wa talakawa wajen aiwatar da ajandarsa mai suna ‘ARISE’.
Bayan koke-koke da ya taso daga wasu fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar PDP da ba sa cikin wadanda aka nada, ya yi alkawarin zai kara nada mukarrabai har 4,000, yana mai cewa za a yi amfani da su ne wajen gudanar da shirin gwamnatinsa.
Wannan na zuwa ne baya ga nada wasu mataimaka 30 da gwamnan ya yi da kwamishinoni 23 da kuma mai ba da shawara na musamman guda daya da aka rantsar a watan Yuli.
An bayyana cewa gwamnatin Jihar Akwa Ibom za ta kashe akalla naira miliyan 73.6 wajen kula da mataimaka 368, saboda kowannen su zai samu na naira 200,000 a duk wata.
Kokarin jin ta bakin kwamishinan yada labarai, Mista Ini Ememobong da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Mista Ekerete Udoh ya ci tura domin ba su amsa kiran waya ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Jihar Filato
A Jihar Filato, gwamna Caleb Mutfwang ya nada sama da mukarrabai 200 da suka hada da, sakataren gwamnatin jihar, kwamishinoni, shugabannin hukumomi, ma’aikatan agaji, masu ba da shawara na musamman.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Musa Adams bai amsa kira ko sako karta kwana ba dangane da wannan batu har zuwa hada wannan rahoto.
Jihar Ebonyi
A Jihar Ebonyi, gwamna Francis Nwifuru ya nada kwamishinoni 35 da mataimaka na musamman guda 40 tun da ya hau mulki a watan Mayu.
Mataimaki na musamman ga gwamna, Boniface Nwankwo ya ce nadin ba domin bayan goyon siyasa ba ne kamar yadda wasu ke tunani a jihar, amma alama ce ta gwamnati mai son jama’a.
“A ranar Laraba, Gwamna Nwifuru ya nada karin mataimaka na musamman guda 5, wanda ya kawo adadin zuwa 40 da kwamishinoni 35.
“Ban ga wani abu da ba daidai ba game da hakan, saboda gwamnanmu ta kasance mai son jama’a,” in ji shi.