Hukumar kula da albarkatun mai na cikin teku da tudu (NMDPRA) ta bayyana cewa, karancin kudaden waje da karyewar darajar Naira ya tilastawa kamfanonin kasuwancin man fetur dakatar da shigo da man fetur.
Haka kuma hukumar ta bayyana cewa, amfaniu da man fetur ya matukar raguwa, inda ya ragu da kashi 33.58, daga lita miliyan 66.7 a kullum kafin a janye tallafin man fetur zuwa lita miliyan 44.3 a kullum a halin yanzu.
- Gobe Za A Tsame Duk Ma’aikacin Tarayya Da Ba Ya Cikin Tsarin IPPIS Daga Biyan Albashi
- Gobe Za A Tsame Duk Ma’aikacin Tarayya Da Ba Ya Cikin Tsarin IPPIS Daga Biyan Albashi
Shugaban hukumar, Farouk Ahmed, ya bayyana haka a jawabinsa yayin taron masu ruwa da tsaki a harkokin man fetur da aka yi a Legas ranar Litinin.
Ya kuma kara da cewa, kamfanonin safarar albarkatun man fetur 8 daga cikin kamfanoni 94 da aka bai wa lasisi suka samu nasarar shigo da jiragen ruwa 8 na man fetrur da ya kai 251,000 MT ( lita 291,238,670.69) a tsakaninwatan Yuni da Satumba na shekarar 2023.
Ya ce, raguwar da aka samu na kamnfanonin da ke shigo da man fetur wajen aikin shigo da man fetur ya faru ne saboda matsalar da kamfanonin suke fuskanta wajen samun kudaden kasashen waje na Dala.
Ya kuma nuna cewa, gwamnati na kokarin ganin ta hade yadda ake bayar da kudaden kasashenwaje ta yadda kamfanonin mai za su samu, ana kuma kokarin ganin an daidaita darajar naira a kasuwannin bayan fage.
“Ana fatan samar da man fetur zai kara tabbata tare da wadata in har matatar man Dangote ta fara aiki aka kuma yi wa matatatr man NNPC garanbawul suka fara aiki yadda ya kamata.
Ya kuma yaba wa kokarin gwamnatin Nijeriya na tabbatar ab samu wadatar man fetur a koda yaushe a fadin kasar a kuma farashin da ya dace.
Ya ce, cire hannun gwamnati gaba daya a bangaren zai taimaka wajen daidaita farashi da kuma karfafa al’ummar Nijeriya sun fara duba yiwuwar amfani da wasu makamashin da ba man fetur ba.