Bayani ya nuna cewa, kamfanoni fiye da 3,030 suka nuna bukatar su na samun lasisin hakar ma’adanai daban-daban da ke shimfide a fadin tarayyar Nijeriya.
Shugaban hukumar kula da hakar ma’adanai na kasa, Mista Obadiah Nkom, ya sanar da haka a takardar manema labarai da aka raba Litinin a Abuja.
- Yadda Na Sha Mugun Duka A Hannun ‘Yansanda — Ajaero
- Sin Za Ta Zurfafa Matakan Kare Ikon Mallakar Fasaha Yayin Bunkasa Ci Gaba Ta Hanyar Kirkire-Kirkire
Sanarwa ta nuna cewa, wadannan kamfanonin na neman izinin mu’amalar hakar ma’adanai fiye 7,310.
Ya ce, kamfanoni 977 sun mika bukatar ta su ne ta hanyar cika ‘Form’ a shafin hukumar na intanet yayin da kuma kamfanoni 2,053 suka mika na su bukatar ga ma’aikatar ma’adanai ta kasa.