A ci gaba da sauraron kararrakin zabe da aka shigar a kotunan daukaka kara da ke Abuja da Legas, an samu bazata a wasu daga cikin hukunce-hukuncen da aka zartar da hukunci a wannan mako, musamman ma a shari’o’in ‘yan majalisa na jiha da kuma na gwamna.
Idan dai za a iya tunawa, an rarraba shari’o’in zuwa bangare guda biyu, inda aka mayar da dukkan shari’o’in zaben da aka daukaka kara na yankin arewa a sashin kotun daukaka kara da ke Abuja, yayin da reshen kotun daukaka kara da ke Legas zai yanke hukuncin dukkanin kararrakin zabe na yankin kudu.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Fatali Da Zargin Da Obi Ya Yi Mata Kan Karin Kasafin Kuɗi
- Gaza: Majalisar Dattawa Ta Nemi Nijeriya Ta Matsa Lambar Kafa Kasashe Biyu
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta kori nasarar Musa Ilyasu Kwankwaso na jam’iyyar APC, a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Kura/Madobi/Garun Malam.
Ta tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar NNPP, Yusuf Umar Datti, a matsayin halattaccen dan majalisa.
A hukuncin da ta yanke mai alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a Tunde Oyebamiji Awotoye, kotun ta tabbatar da nasarar Datti, wanda tun farko hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zabe.
Sai dai kuma kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Jihar Kano, ta bai wa Kwankwaso nasara.
Mai shari’a Awotoye cewa kotun sauraron kararrakin zabe ta yi kuskure. Alkalin ya lura cewa an yi amfani da sashe na 77 na dokar zabe. Ya ce babu wata kotu da ke da hurumin yin kasalandan a rikicin cikin gida na jam’iyya.
A bangare guda kuma, kotun daukaka kara reshen Jihar Legas ta kuma kori Darlington Nwokocha, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, mai wakiltar Abiya ta tsakiya a karkashin jam’iyyar LP.
Kotun ta bayyana Augustine Akobundu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu na yankin majalisar dattawa.
Yayin da kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kuma kori tsohon gwamnan Jihar Benuwai, Gabriel Suswam daga majalisar dattawa.
Kotun ta ayyana Mista Emmanuel Udende na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara.
Haka kuma kotun daukaka kara da ke Abuja ta kuma kori Sanata Ishaku Abbo, dan majalisa mai wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dattawa, wanda ta ayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Amos Yohanna a matsayin wanda ya yi nasara.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kuma kori dan majalisa mai wakiltar Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu da kuma Maiha ta Jihar Adamawa a zauren majalisar wakilai, Hon. Jingi Rufai.
Kotun ta kori dan takarar jam’iyyar PDP a zaben majalisar, yayin da ta bayyana Hon. Jaafar Magaji na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar kuma ta umurci INEC da ta ba shi takardar shaidar cin zabe.
Sai dai kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da Natasha Akpoti-Uduagan, ‘yar takarar jam’iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe zaben Sanatan Kogi ta Tsakiya da aka gudanar a farkon watan Fabrairu.
Kotun ta yi watsi da karar da Sanata Abubakar Sadiku Ohere na jam’iyyar APC ya shigar saboda rashin cancantata.
Kotun ta Abuja ta kuma yi watsi da wani hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke a Jihar Adamawa, ta tabbatar da Mohammed Salihu a matsayin wanda ya lashe zabe a karkashin tutar jam’iyyar PDP a matsayin dan majalisar wakilai.
Haka zalika, kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kammala sauraron karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar domin kalubalantar tsige shi da kotun sauraron kararrakin zabe ta yi a Jihar Kano.
Alkalan kotun sauraron kararrakin zabe mai mutum uku karkashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay, suka sauke nasarar Abba a ranar 20 ga Satumba, 2023, inda suka bayyana cewa kuri’u 165,663 ba su da inganci, saboda babu sa hannun INEC kuma babu sitamfin.
Daga nan sai aka rage kuri’un gwamnan zuwa 853,939, yayin da Ganuwa ya samu kuri’u 890,705.
Gwamna Abba ya ki amincewa da hukuncin kotun, wanda ya bayyana a matsayin “Rashin adalci”, inda ya garzaya kotun daukaka kara.
A zaman kotun na ranar Litinin, jagorar lauyoyin gwamnan, Wole Olanipekun, ya bukaci a yi watsi da hukuncin kotun sauraron karar zabe.
Da yake nuna adawa da hukuncin da aka yanke a kan kuri’un bogi, babban lauyan ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihi da kotun sauraron karar zabe ta soke zaben da aka yi kan rashin sanya hannu a bayan kuri’un da aka kada lokacin zabe.
Sai dai lauyan APC, Akin Olujimi, ya ki amincewa da bukatarsa, yana mai cewa kotun daukaka kara ta bayyana karara cewa rashin sanya hannu kan kuri’u ya kasance hanyar yin magudin zabe.
Ya kara da cewa dokokin INEC sun bayyana cewa dole ne kowacce kuri’a a sanya hannu tare da rubuta kwanan wata a wata.
Daga karshe kotun daukaka kara ta ce za a sanar da ranar yanke hukunci ga dukkan bangarorin.