Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bada hakuri kan gaza kwashe dukkan maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya domin aikin Hajjin bana da ala gudanar a ranar Juma’a.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa maniyyata 1,551 ne, daga jihohi 3 da kuma na kamfanonin sufuri basu samu zuwa aikin Hajjin bana ba.
A wata sanrwa da NAHCON ta fitar, mai dauke da sa hannun jami’ar hulda da jama’a, Fatima Sanda Usara, hukumar ta ce maniyyata tara daga jihar Bauchi; 91 daga jihar Filato; 700 daga jihar Kano da kuma kimanin 750 daga bangaren kamfanonin sufuri ne basu samu zuwa aikin Hajjin ba.
A sanarwar, NAHCON ta nuna takaicin faruwar lamarin, inda ta bai wa wadanda abun ya shafa hakuri.
Hukumar ta kuma yi alkawarin mai da wa kowa kudin da ya biya, inda ta bayyana cewa ta dauki darussa masu yawa a kan matsalar da a ka samu, ta kuma ci alwashin gyara wa a shekaru masu zuwa.
“Abin takaicin shi ne, duk da kokarin da aka yi na jigilar dukkan maniyyatan Nijeriya da ke son zuwa kSaudiyya don gudanar da aikin Hajjin 2022, NAHCON ta gaza wajen sauke wannan nauyi, musamman sakamakon koma bayan da aka samu a karshen makon da ya gabata da ya kawo cikas ga shirinta na kammala jigilar maniyyatan zuwa ranar 27 ga watan Yunin wannan shekara.
“Sai dai abin takaicin shi ne, zabin jirage da aka yi hayar da ya bai wa hukumar NAHCON da kuma masu gudanar da jigilar maniyyatan kamfanonin yawon bude ido masu zaman kansu su ma ya ci tura saboda asusunsu na IBAN ya gaza samun amincewar hukumomin Saudiyya.
“Musamman, wadannan adadin maniyyatan da abin ya shafa ba za su je Saudiyya kafin rufe filin jirgin sama na Jeddah ba, don haka za su yi Hajjin bana. Su ne: Mahajjata tara (9) daga jihar Bauchi; Alhazai 91 daga jihar Filato; Mahajjata 700 ne daga jihar Kano da kuma mahajjata kimanin 750 daga bangaren masu yawon bude ido masu zaman kansu,”