Shekaru bayan kaddamar da shirin samar da tasoshin teku na kan-tudu a sassan kasar nan har zuwa yanzu da dama daga cikinsu ba su fara aiki ba, ballantana a fara cin gajiyar su.
Binciken da LEADERSHIP ta yi, ya nuna cewa, tashar teku ta kan-tudun da aka samar a wasu jihohin kasar suna nan sun lalace bayan da aka narka biliyoyin naira don tabbatar da aikin ya samu nasarar da ake bukata.
- Harin Filato: Gwamnati Ba Za Ta Huta Ba Har Sai An Hukunta Maharan – Shettima
- Ganduje Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Na’Abba
A yawancin garuruwan da aka kafa wadannan tasoshin tekunan an yi wa dubban matasan yankin alkawarin samun ayyukan yi wanda har zuwa yanzu babu wani fata na yiwuwar hakan. Haka kuma an lasa wa al’ummar yankunan zuma a baki a kan bunkasar tattalin arziki da ingantuwar rayuwa.
Gwamnatocin jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Borno, Filato da Oyo sun samar da dubban hektoci na filaye ga gwamnatin tarayya amma saboda tsananin rashin cikakken shiri da gudanar da aiki tare tsakanin gwamnatocin jihohin da ma’aikatun gwamnatin tarayya da suke da hannu a kan lamarin har zuwa yanzu ba a kai ga samun nasarar da ake bukakata ba a kan shirin.
A watan Maris na shekarar 2006 ne majalisar zartaswar gwamnatin tarayya ta amince da a samar da tasoshin teku na kan-tudu a sassa 6 na tarayya Nijeriya wadanda suka hada da Isiala-Ngwa a Jihar Abiya; Erunmu Ibadan – a Jihar Oyo; Heipang Jos – a Jihar Filato; Funtuwa- a Jihar Katsina; Maiduguri – a jihar Borno da kuma Dala a Jihar Kano.
Amma kuma tashar kan-tudu ta Kaduna da ba a sa a cikin tsarin farko na guda shida da aka yi shekarar 2006 ba, ta samu tagomashin kaddamarwar gwamnatin tarayya a shekarar 2018, an kuma yi haka ne don ya zama wurin da za a rika sauke kayayyakin da suka nufi kasashen da ba su da tasoshin ruwa da ke makwabtaka da Nijeriya kamar kasashen Nijar da Chadi, ta haka za a samu sakin safarar kayayyaki a tsakanin kasashen.
Tashar kan-tudu ta Kaduna ta fara gabatar da kwaryakwaryar aiki amma rashin kammala aikin hanyar jirgi yana kawo cikas ga zirga-zirgar kayayyaki daga tasoshin ruwan Nijeriya zuwa tashar kan-tudu ta Kaduna, kamar yadda bincike ya nuna.
Wakilinmu da ya ziyarci tashar ta Kaduna da ke unguwar Kakuri kusa da tashar jirgin kasa, inda ya lura da cewa wasu manyan motoci kalilan ake iya gani suna dauka da sauke kayayyaki a tashar a rana.
An kiyasta tashar na da karfin mu’amala da kayyakin da suka kai tan 29,000 a duk shekara, sannan za ta kuma iya samar da ayyukan yi ga mutum fiye da 5000.
A jihar Filato kuma, shekara 17 bayan kadamar da tashar kan-tudu na Heipang, da ke karamar hukumar Barikin Ladi da tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya yi har yanzu ba a fara wani aiki a tashar ba.
Haka kuma a watan Fabrairu na shekarar 2023 ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da tashar kan-tudu da ke Funtuwa a Jihar Katsina, inda ake sa ran ta zama masaukin manyan kayayyaki da kwantainonin da aka shirya fitarwa zuwa kasashen waje.
Tun bayan kaddamar da tashar har zuwa yanzu ba a kai ga fara aiki a tashar ba, ministan sufuri, Mu’azu Jaji Sambo ya jagoranci kaddamar da tashar.
Binciken da wannan jaridar ta yi ya nuna cewa, tashar na nan ba a aikin komai, sai da an fahimci wasu sun manyar da tashar wajen ajiye kayayyaki zuwa wani lokaci su kwashe abin su, duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin shugaban tashar ya ci tura.
Haka kuma a watan Agusta na shekarar 2022, gwamnatin tarayya ta kaddamar da tashar kan-tudu ta Kano da ke Dala, don ta kasance wurin saukar da kayayyaki da suka fito daga tasoshin Ruwan Nijeriya.
…Tashar Baro Ba Labari, Ciyayi Sun Mamaye, Ruwa Na Raruke Gabar Kogin
Ciyayi da sauran tsirrai suka mamaye tashar jiragen ruwa na biliyoyin naira a garin Baro ta Jihgar Neja wanda tsohon shhugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a shekarar 2019. A halin yanzu ma ruwa na ci gaba da cin gabar kogin har ya fara neman isa gine-ginen da aka yi na tashar.
Binciken da LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa, gine-ginen da aka yi na tashar da sauran ayyukan da kwararru suka samar ya lakume wa gwamnatin tarayya naira biliyan 3.5, wannan bai hada da kudin yashe kogin ba don ba a sanya shi ba a ciki a lokacin da aka kaddamar da aikin.
Binciken ya kara nuna cewa, ciyawa da sauran tsirrai sun mamaye harabar tashar ce saboda tun da aka kaddamar da tashar ba a yi wani aiki ko guda daya ba a wurin duk kuwa da cewa, gwamnati ta yi alkawarin gudanar da aiki nan take a tashar a yayin kaddamarwar.