Super Eagles ta samu nasarar doke kungiyar Al Gharbia FC da ke kasar Dubai da ci 12-0 a wani wasan sada zumunta da suka buga a Abu Dhabi ranar Lahadi.
Kwallayen sun fito daga Osimhen da Musa da Sadiq da Lookman da Moses Simon inda suka lallasa kungiyar da ke buga rukuni na uku a gasar kwallon kafa ta kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
- Zamu Dogara Da Osimhen Don Lashe Gasar AFCON – Peseiro
- AFCON 24: Yusuf Alhassan Ya Maye Gurbin Ndidi A Cikin Tawagar Yan Wasan Nijeriya
Koci Jose Peseiro ya yi canje-canje da yawa domin gwada dukkan yan wasan gabanin fara wasan farko na AFCON da Equatorial Guinea ranar Lahadi mai zuwa.
Za a fara gasar ta AFCON karo na 34 a ranar 13 ga watan Janairu kuma za a kammala gasar a ranar 11 ga watan Fabrairu.