Yanzu haka dai daya daga cikin batutuwan da suka fara tayar da sabuwar kura a farfaijiyar siyasar Jihar Kano shi ne batun makomar masarautun da tsohuwar gwmanatin Abdullahi Umar Ganduje ta kirkira guda hudu da suka hada da Bichi, Rano Gaya da Karaye, bayan warware rawanin tsohon Sarkin Kano na 14, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi.
‘Yan Kwankwasiyya na ta shelanta cewa tun da Allah ya ba su wannan dama za su dawo da korarren sarkin, wanda kuma dawowarsa za ta iya zama silar sauke wadancan sarakuna hudun ko makamancin hakan.
- Kofin Afirka 2023: Yadda Manyan Kasashe Ke Tafka Abin Kunya
- Ya Kamata Sin Da Faransa Su Ba Da Jagora Wajen Yin Mu’amala A Shekaru 60 Masu Zuwa
 An sha jin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso mai juya akalar jam’iyyar NNPP a Kano na cewa, abubuwan da suka alkawarta wa Kanawa a lokacin yakin neman zabe dole su cika su, kuma jam’iyyar ta fara cika alkawari ta hanyar rushe wasu wuraren da suka bayyana cewa an yi ba bisa ka’ida. Haka suma ma’aikatan da Gwamnatin Ganduje ta dauka guguwar wannan sauyi ta yi awon gaba da su.
Ana cikin wannan hali ne kuma kwatsam sai jagoran Kwankwasiyyar ya gabatar da wata hira a kafafen yada labarun Jihar Kano, wanda a cikin tattaunawar aka tambayeshi batun matsayin sarakunan hudu da ake ta ce-ce-ku-ce a kansu, nan take ya bayyana cewa, “Ni ba a yi kowone irin zama kan haka da ni ba, amma dai na san dole za mu zauna mu duba abin da ya kamata a gyara, sai a gyara wanda kuma za a bari sai a bari.
 Ra’ayoyin Mutane…Â
Daya daga cikin masu adawa da Gwamnatin Kwankwasiyya, Danbilki Kwamanda ya gabatar da nasa jawabin wanda kuma ya soki gwamnati kan maganar masarautu.
Sai dai wannan kalamai ya sa an kama Kwamanda Danbilki bisa zargin za su iya tunzura al’umma wadanda suka shafi batun masarautun Kano.
Hukumar DSS ce ta fara gayyatarsa tare da mika shi ga jami’an rundunar ‘yan sanda, kamar yadda lauyan da ke kare shi, Barriser Ibrahim Abdullahi ya tabbatar wa da manema labarai a Kano.
Shi ma mai bai wa gwamna shawara kan harkokin addinai II, Gwani Musa Hamza Falaki ya yi karin haske kan ce-ce-ku-ce-cen da ke ta kara ruruwa kan batun masarautun Kano. Ya ce a bangaren Gwamnatin Abba har yanzu lokaci bai yi ba, kuma ba inda ya taba bayyana shirin cire wadancan sarakuna, domin akwai matakai da kowacce gwamnati ke bi wajen warware duk wata matsala da kalubale.
Ya ce Kanawa kowa ya sha kuruminsa domin Gwamnatin Abba babbu abin da ke gabanta illa ci gaban Kanawa, saboda haka duk abin da zai taimaki wa al’umma shi ne babban burin wannan gwamnatin.
A bangaren Amb. Mansur Haruna, wanda yana daga cikin ‘yan jam’iyyar adawa ta APC wadanda suke kallon yunkurin wannan gwamnati bai wuce batun tsige sarakunan da al’umma ke matukar farin ciki da zuwansu ba.
A cewarsa, jama’a sun ga irin ci gaban da aka samu sanadiyyar nada wadannan sarakuna. Ya ce yanzu an ji maganar da jagoaran Kwankwasiyyar ya yi wanda kuma duk abin da ya fada dole shi suke zaton zai faru, saboda haka su a ganinsu sun gama shirye-shiryen tsige wadannan sarakuna da ke zaman alkairi ga Kanawa.
Wadannan su ne abubuwan da a halin yanzu a Jihar Kano ke fuskanta, musamman ganin yanzu gwamantin ta zauna, kuma su akidar Kwankwasiyya ita ce, fada da cikawa. An dai ji kalaman su, inda suke jadadda cewa dukkan alkawuran da suka yi lokacin yakin neman zabe suna kyautata zaton cikawa, har ma sun fara nuna irin wannan matsaya kan wasu kasuwannin Jihar Kano da ma’aikatan da gwamnatin baya ta dauka aiki da kuma batun masarautu, wanda yanzu su ne lamarin da ya fi tayar da hankali a farfajiyar siysar Kano.
Abin da masana ke kokarin nunawa bai wuce ita gwmanatin Abba ta yi kokarin rike matsayinta, sannan kuma ta fuskanci kalubalen da ke gabanta domin guje wa barin jaki a koma dukan taiki.