• English
  • Business News
Sunday, June 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin Gwamnati Na Samar Da Mafi Karancin Albashi

by Leadership Hausa
1 year ago
in Ra'ayoyi
0
Shirin Gwamnati Na Samar Da Mafi Karancin Albashi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin mutum 37 don duba lamarin samar da mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar nan, an ba kwamitin umarnin tabbatar da fitar da tsarin mafi karancin albashi tare da la’akari mastalolin da al’ummar Nijeriya kie fuskanta a bangaren tattalin arziki da sauransu. A ra’ayinmu wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci, an kuma umarci ‘yan kwamitin su fito da mafi karancin albashin da zai samu karbuwa ga dukkan matakan gwamnati. An kuma nemi su yi nazari tare da fitar da dalilan da ya hana wasu jihohi aiwatar da mafi karancin albashin da aka aiwatar a baya.

In aka lura da wanann umarnin daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu za a fahimci cewa, shugaban kasa ya damu da al’amarin matsin rayuwu da ya shafi ma’aikatan gwamnati ne kawai. Amma in aka lura za a iya fahintar cewa, wannan ba karamin kuskure ba ne, don ya kamata a ce an samar da wata mafita ga ma’aikata masu aiki a bangaren kamfanoni masu zaman kansu domin suma suna fuskantar matsin rayuwa da dukkan ‘yan Nijeriya ke fuskatanta.

  • Tsadar Rayuwa: Majalisar Wakilai Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Lalubo Mafita
  • Cire Tallafin Fetur: Ma’aikatan Jihar Jigawa Sun Ki Amincewa Da Karin Albashin Naira 10,000

Amma kuma a ra’ayinmu, ya kamata a fahinci cewa, ‘yan Nijetriya da suke aiki a kamfanoni masu zaman kansu suma suna fuskantar matsalolin tattalin arziki da tsadar rayuwar da ake ji a halin yanzu. Haka kuma wadanda ma basa wani aiki na gwamnati ko kuma ma masu zaman kansu suma suna fatan gwamnati ta sa su a lissafi ta yadda za su samu jin saukin tashin farashin kayayyaki da zai faru in an kara wa ma’aikata albashi.

Zuwa yanzu, bangarorin da ya ke tattaunawa a kan mafi karancin albashin sun fara ayyana wasu manyan kudade da ba zai a iya aiwatarwa ba. A ra’ayinmu, maimakon a ayyana wani albashi masu yawa wanda ba za a iya aiwatarwa ba, daga kaarshe abin ya tsaya kawai a takardar ba tare da an iya aiwatarwa ba. ya kamata a samar da tsarin da zai samu karbuwa ga dukkan bangarori. Ya kuma kamata a cire dukkan abin da ya shafi siyasa da son rai wajen aiwatar da mafi karancin albashin, musamman ganin irin wahalar da al’umma ke fama da shi a wannan lokacin.

A sharhin da muka gabatar a baya mun nemi a kara wa ma’aikata albashi, albashin da zai dauki dawainiyar rayuwar ma’aikaci. Za kuma mu ci gaba da da’awar neman a a tabbatar da an kara wa ma’aikacin Nijeriya albashi. A bayyana yake cewa, duk irin kudin da aka biya mai karbar albashi ba zai taba isansa tafiyar da raywuarsa ba.

Labarai Masu Nasaba

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

A cikin sharhin da muka yi mun nemi gwamnati ta sa hannu a dukkan bangarorin rayuwar al’umma Nijeriya gaba daya ba wai na masu karbar albashi kawai ba, al’amarin ba kawai na albashi ba ne, harma na abin da albashin zai iya saya.

Wannan ne ya kawo mu a kan bukatar a gagguta sake fasalin albashi da tattalin arzikin kasa baki daya. Ta yadda za a samu saukin farashin kayan masarufi. Duk da cewa, babu yadda albashi zai iya biya wa ma’aikaci bukatarsa amma albashin ya zamana zai iya raka ma’aikaci zuwa wani mataki mai muhimmanci a duk wata.

A ra’ayinmu duk yawan albashin da za a ba ma’aikaci a karshen wata ba zai taba isarsa ba in har aka ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi.

Yana da muhimmanci mu jawo hankalin gwamnati a kan tsadar kudin sufuri wanda a halin yanzu gwamnati ta bari a hannun bangarori masu zaman kansu, wanda suke amfani na lallacewar hanyoyinmu da hauhawar farashin albarkatun man fetur wajen tsawwala farashin kudin mota. A yayin da babu tsarin sufuri na gwamnati, kudaden sufurin da ma’aikaci zai ci gaba da kashewa zai ci gaba da hauhawa a waasu lokutta ma ba zai iya biya ba saboda tsada, duk kuwa da yawan albashin da gwamnati za ta ba ma’aikaci.

A bangaren kiwon lafiya, ‘yan Nijeriya da ke aiki a bangaren gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu ba su da wani tsarin kula da lafiya da zai tabbatar da kula da lafiyarsu dana iyalansu. Asibitocin gamnati da ake da su suma suna gwa-gwa ne da asibitoci masu zaman kansu wajen tsada.

Haka kuma, a kullum sai ka ji gwamnati na bayanin wai muna da gibin gidaje fiye da miliyan 16 amma kuma har yanzu bamu ga abin da ta yi ba don magance lamarin. A bangaren ilimi kuma, kusan gwamnati ta saki makarantu a dukkan mataki ga hannun masu zaman kansu.

A bayyana yake cewa, harkokin kasuwanci na tafiya a kasar nan ne tamkar babu gwamnati, ‘yan kasuwa sun zama gwamnatin kansu ta hanyar samar wa kansu abubuwan tafiyar da harkokinsu kamar, hanyoyi, ruwa, wutar lantarki da sauransu. Gwamnati na tuna dasu ne kawai in lokacin karbar haraji ya yi amma ba wai a yi muusu ayyyukan da zai sa su ji dadin tafiyar da harkokin kasuwancinsu ba.

Wadanan ko-in-kular ke kara zama kalubale ga tattalin arziki, musamman shi ne ke karya darajar kudin da ake karba da sunan albashi. Dole a ba gwamnati shawarar mayar da hankali a kan daukar matakan tabbatar da tattalin arzkin kasa yana tafiya. A ra’ayinmu, in har ana bukatar a samu ma’aikatan gwamnati da za su bayar da gudumawarsu wajen gina kasa dole a samar da tsarin tattalin arzikin tare da yaki da hauhawar farashi in ba haka duk karin albashin da za a yi zai zama matakin karin wahala ne kawai ga ma’aikata da sauran al’ummar Nijeriya.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Abuja Na Fuskantar Baranazar Tsaro -Majalisar Dattawa

Next Post

Goron Juma’a

Related

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 
Ra'ayoyi

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

3 months ago
Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri
Ra'ayoyi

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

8 months ago
Nijeriya
Ra'ayoyi

Ra’ayoyin ‘Yan Nijeriya A Kan Zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai

9 months ago
Shekara 64 Da Samun ‘Yanci: Maimakon Biki, Jajantawa Ya Kamata A Yi – ‘Yan Nijeriya
Ra'ayoyi

Shekara 64 Da Samun ‘Yanci: Maimakon Biki, Jajantawa Ya Kamata A Yi – ‘Yan Nijeriya

9 months ago
Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Gwamnatin Tarayya A Kan Tozarta Marasa Lafiya Daga Jami’an FIRS A Kano
Ra'ayoyi

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Gwamnatin Tarayya A Kan Tozarta Marasa Lafiya Daga Jami’an FIRS A Kano

9 months ago
Dauda Lawal A Shekara 59: Mai Gidana Wanda Bai Da Jiji Da Kai
Ra'ayoyi

Dauda Lawal A Shekara 59: Mai Gidana Wanda Bai Da Jiji Da Kai

10 months ago
Next Post
Goro

Goron Juma’a

LABARAI MASU NASABA

Madarar Shanu Da Nijeriya Ke Samarwa Ta Karu Da Tan Miliyan 1.4 A Shekara Biyar

Madarar Shanu Da Nijeriya Ke Samarwa Ta Karu Da Tan Miliyan 1.4 A Shekara Biyar

June 29, 2025
Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda

Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda

June 29, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100

Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100

June 29, 2025
Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki

Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki

June 29, 2025
Kasar Sin Ta Sake Ware Yuan Miliyan 100 Domin Tallafawa Lardin Guizhou Dake Fama Da Ambaliya 

Kasar Sin Ta Sake Ware Yuan Miliyan 100 Domin Tallafawa Lardin Guizhou Dake Fama Da Ambaliya 

June 28, 2025
An Kaddamar Da Aikin Hadin-Gwiwar Kafafen Yada Labaran Sin Da Kasashen Waje Wajen Watsa Labarai Game Da Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Kaddamar Da Aikin Hadin-Gwiwar Kafafen Yada Labaran Sin Da Kasashen Waje Wajen Watsa Labarai Game Da Jihar Xizang Ta Kasar Sin

June 28, 2025
Jakadun Kasa Da Kasa Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwa Wajen Amfani Da Makamashin Nukiliya Ta Hanyar Lumana

Jakadun Kasa Da Kasa Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwa Wajen Amfani Da Makamashin Nukiliya Ta Hanyar Lumana

June 28, 2025
Kokarin Zamanantar Da Sin Da Afrika Na Kara Karfafa

Kokarin Zamanantar Da Sin Da Afrika Na Kara Karfafa

June 28, 2025
Bashin Da Ake Bin Nijeriya Ya Kai Tiriliyan 46.25

Za A Ci Gaba Da Tunawa Da Aminu Ɗantata A Ɓangaren Taimakon Jama’a — Buhari

June 28, 2025
Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

June 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.