Masu zuba jari a bangaren ma’adanai sun nuna aniyarsu na zuba jarin fiye da Dala Biliyan 20 don bunkasa harkar hakar ma’adanai a fadin tarayyar Nijeriya wanda hakan zai taima wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Shugaban kamfanin hakar ma’adanai na ‘Daroo Nigerian Limited” Alhaji Mohammed Abba Liman, ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja ranar Litinin.\
- Lokaci Ya Yi Da Za A Kawo Karshen Musguna Wa Fulani – Dakta Awwal
- Shugaban Miyetti Allah, Abdullahi Bodejo Mutum Ne Mai Yi Wa Nijeriya Fatan Alhairi
Ya kuma kara da cewa, kamfanonin sun nuna sha’awarsu ne na hakar ma’adanai kamar su lithium, lead, gwal, da sauran ma’adanai da ke shinfide a sassan kasar nan.
Ya kuma kara da cewa, gwamnati na samar da shirye-shirye mai dorewa don bunkasa bangaren ma’adanai na kasa ta yadda al’umma za su amfana.
“Abokan huldar za su fito ne daga kasashen Birtaniya, Saudi Arabiya, Turkiya, Chana da kuma Farasa,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa, kamfanin ‘Daroo Nigerian Limited’ na hadin gwiwa ne da ma’aikatar ma’adanai na kasar Saudi Arabiya. Ya ce hukumar kasar Saudiya ta bayanna cewa, duk kamfanin Nijeriya da ke sha’awar yin huldar hakar ma’adanai da kamfanonin kasar Saudiya yana iya neman izinin yin haka ta hannun kamfanin tace gwal na kasar Saudiya mai suna ‘Saudi Gold Refinery Company Ltd’ da ke Riyadh.
Liman ya kuma ce, wannan sha’awar na shiga harkar hakar ma’adamai da aka samu daga kasar Saudiya ya faru ne sakamakon taron bunkasa ma’adanai da kasar Saudiya ta dauki nauyin gabatarwa a watan Disamba na shekarar 2023, inda ministan ma’adanai na Nijetiya Dr Dele Alake, ya jagoranci tawagar Nijeriya.