Wata Kungiya mai zaman kanta (NGO), Dove-Haven Foundation (DHF) ta ce sama da mutane miliyan 2.3 a halin yanzu ke fama da cutar kansar nono sannan kuma mutane 700,000 ne suka mutu sanadiyyar cutar a duk fadin duniya. Daily trust ta rahoto
Babban daraktan hukumar ta DHF, Dakta Ekundayo Samuel ne ya bayyana hakan a Isanlu, dake karamar Hukumar Yagba ta gabas a jihar Kogi, inda ya ce ciwon dajin-mama yanzun shine Kan gaba fiye da kansar Huhu da ta dade tana addabar al’umma a duk duniya.
“A Nijeriya, ya zuwa yanzun, a cikin shekaru biyar, hudu daga cikin biyar masu fama da cutar daji yana wuya su tsira daga cutar,” in ji shi, ya kara da cewa duk da rashin samun cikakkun bayanai daga cutar, dajin-mama har yanzu shi ne kan gaba a nau’in ciwon daji a Nijeriya dake azabtar wa kuma mutane da yawa suna rasa rayuwarsu sanadiyyar cutar kowace shekara.
Dakta Samuel ya ci gaba da cewa DHF ta kasance daya daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu da suka mayar da hankali kan cutar kansa, musamman mun fi mayar da hankali a yankunan karkara saboda imanin mu na cewa mutanen karkara suma suna da hakkin samun damar samun tallafin kula da cutar kansa.
Shugaban kungiyar masu fama da cutar daji ta Nijeriya, Dakta Alhassan Umar Adamu, ya bayyana cewa Nijeriya tana da Karancin kwararrun Likitoci da zasu iya tunkarar adadin masu fama da cutar dajin a Nijeriya.