Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu a kauyen Nkienzha da ke Miango a masarautar Irigwe ta karamar hukumar Bassa a jihar Filato.
LEADERSHIP ta rawaito cewa ‘yan bindigar sun kai hari a unguwar da misalin karfe 11 na daren ranar Lahadi inda suka kone wani gida da kashe wasu mutane hudu a cikin yayin kai harin.
- Gwamnatin Filato Ta Kafa Kwamitin Mutane 10 Don Shawo Kan Matsalar Tsaro
- Rikicin Filato: Atiku Ya Koka Kan Rashin Kwazon Jami’an Tsaro
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Cigaban Irigwe ta kasa (IDA), Davidson Malison, ta ce an samu wani mutum guda ya samu raunika.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, shugabancin kungiyar ta Irigwe ya ce kai hare-haren a matsayin rashin tausayi, ta kuma yi gargadin masu aikata wannan da irin wannan rashin imanin.
Kungiyar ta yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar sun kama wadanda suka aikata wannan ta’asar tare da gurfanar da su a gaban kuliya.