• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nazari A Kan Kiwon Talo-Talo A Takaice

by Abubakar Abba
2 years ago
Kiwon

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

A faninin kiwon Talo-talo a Nijeriya, ana matukar samun dimbin riba, har ila yau kuma fanni ne wanda ya ke daidai da sauran fannin kiwon sauran dabbobi, indai har an fara yin sa yadda ya dace.

Kafin gwamnatin tarayya ta haramta shigo da namansa cikin kasar nan, ana yawan shigo da naman nasa cikin Nijeriya kusan a kullum, inda hakan ya jawo raguwar sayen wanda ake da shi a cikin wannan kasa.

  • Ba Za A Iya Dakatar Da Dunkulewar Kasar Sin Ba
  • Dokar Hana Sayar Da Burodi Mara Shaida, Litar Mai Fiye Da 50 Ta Tabbata A Zamfara, Gwamna Dauda Ya Sa Hannu

Shin Kwana Nawa Talo-Talo Yake Kaiwa Kafin Ya Girma?

Talo-talo na kai wa tsawon sati talatin kafin ya girma, sannan yana yin akalla Kwai daga tamanin zuwa dari tare da fara kyankyashe su a cikin kimanin kwana ashrin da takwas, nauyin mata a cikin sati ashirin na kai wa; 4.5 zuwa 5, nauyin maza kuma yana kai wa daga 7 zuwa 8.

Tanadar Kayan Kiwonsa:

Ya kamata a samu kwararru a fannin, wadanda za su gina gurin da za a fara kiwonsu tare da sama musu wajen da za su rika samun wadatacciyar iska, sannan ya kamata kayan da za a yi amfani wajen gina musu dakin kwanan ya kasance ya dace da canjin yanayi,  har ila yau kuma tare da samar musu abinci da kayan shan ruwa.

Tanadar Musu Da Abinci:

Ko shakka babu, Talo-talo na da mutukar cin abinci; wannan dalili ne yasa, wajibi ne wanda zai fara kiwonsu ya tabbatar da ya tanadar musu da abinci mai yawan gaske, domin idan suna samun abinci akai-akai suna yin saurin girma, haka nan ana son mai yin wannan kiwo nasu; ya rika sama musu abincin da ke dauke da sinadarin da ke gina musu jiki, musamman domin su kara samun kuzari tare da samar da Kwai mai tarin yawa.

Samun Ilimin Kiwon Talo-talo:

Yana da matukar kyau a tuntubi kwararrun da ke wannan fanni, domin samun ilimi a kan wannan kiwo na Talo-talo ko kuma a gudanar da bincike a cikin fannin, musamman domin kaucewa yin kuskure, musamman idan za a yi kiwon don kasuwanci.

Amfanin Kiwon Talo-talo Da Kuma Hadarin Da Yake Fuskanta:

Babu shakka, kiwonsa na da matukar alfanu,  musamman ganin yadda ake samun dimbin riba tare da samun wadataccen nama. Kazalika, hanya ce da ke samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa tare da kara habaka tattalin arzikin kasar baki-daya.

Akwai kuma wasu kwari da suke iya yi musu illa,  musamman a lokacin da suke kanana, saboda haka; ana so mai kiwon nasu ya tabbatar yana ba su irin kulawar da ta dace,  har ila yau kuma; akwai kwayoyin cutar da za su iya harbin su, musamman a lokacin da suke kanana.

Bugu da kari, kiwon Talo-talo ba shi da wata whala, musamman idan aka samar da kayan da suka dace wajen kiwon nasu tare da samar da wajen da ya fi dacewa a kiwata su, haka nan ana samun kasuwanni da dama da ake sayar da su.

Shin Kamar Ribar Nawa Mai Kiwonsu Zai Iya Samu?

Ya danganta da yadda girmansu yake, domin babbar mace daya ta Talo-talo a Nijeriya, za a iya sayar da ita kan farashin daga Naira 17,000 zuwa 18,000.

Haka nan, macen Talo-talo daya na iya kyankyashe Kwai daga 10 zuwa 15; matukar suna samun kulawar da ta dace.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Kotu Ta Hana Miji Magana Da Matarsa Tsawon Mako Biyu

Kotu Ta Hana Miji Magana Da Matarsa Tsawon Mako Biyu

LABARAI MASU NASABA

Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya

Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya

October 10, 2025
Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

October 10, 2025
Nijeriya

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
Kiwon

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.