Tun daga tasowata, kalmar dimokuradiyya take burge ni, saboda yadda ake yayata ta a kafafen labarai a Nijeriya sakamakon fafutukar mulki da aka yi tsakanin sojoji da ’yan siyasa har kuma zuwa lokacin da na shiga babbar makarantar sakandare aka koyar da ni ma’anarta a ilmance.
Kusan duk dan ajinmu da ya karanci fannin fasaha (art) idan ka tambaye shi ma’anar dimokuradiyya, bayanin farko mafi sauki, zai kawo maka maganar shugaban Amurka na 16, Abraham Lincoln, “Dimokuradiyya ita ce gwamnatin jama’a da jama’a suka samar kuma domin jama’a.”
- Kafa Jam’iyyar Adawa: Atiku Da Wasu Sanatoci Sun Sake Sabon Yunkuri
- LEADERSHIP Ta Jinjina Wa Shehu Isma’ila Mai Diwani Kan Shafin Dausayin Musulunci
Daga wannan na fahimci, dimokuradiyya tsari ce da ta bai wa al’umma ’yancin samar wa kansu mafita cikin walwala a kan komai ba tare da katsalandan daga ’yan baya ga dangi ba. Wannan ’yanci ba kawai a bangaren mulki ba, hatta a zaman tare tsakanin jama’a mabanbanta kabila da addini.
Da irin wannan ’yanci na dimokuradiyya a duniya, kasashen duniya a nahiyoyi daban-daban suka rika zabar wa kansu tsarin shugabanci da ya dace da su bisa la’akari da yanayin kasarsu da al’ummominsu. Wannan ta sa wasu kasashe suka rungumi mulkin gado na sarakuna kamar Ingila, Saudiyya, Morocco da sauransu. Wasu kuma suke da tsari na samar da shugabanni ta hanyar kuri’a. Wannan kuri’a kuma ba dole sai ta tsarin da wata kasa daya tilo ta amince da shi ba kamar yadda Amurka take karfa-karfar a bi tsarinta a duniya.
Matukar ana son gaskiya da adalci, babu ta yadda za a yi a tilasta wa wata kasa a duniya bin tsarin wata kasa da babu alaka ta tarihi ko makwabtaka a tsakaninsu.
Shi ya sa dimokuradiyya ta zamo tamkar abinci. Abin da wani ya dauka a matsayin abinci, wani na iya ganinsa a matsayin guba saboda bambancin halitta da yanayi. Misali, za ka iya samu a cikin iyalin mutum daya, uwa daya uba daya, amma suna da bambancin abinci. Wani yana cin wake, wani ba ya ci, wani yana shan kunu, wani ba ya sha, hatta nama akwai wanda na san ba ya ci kwata-kwata amma ’yan uwansa da iyayensa duka suna ci. Yanzu idan aka tilasta masa cewa sai ya ci, hakan na iya sanadin rasa rayuwarsa.
To haka dimokuradiyya take, tun da Allah bai halicci mutane iri daya ba, to dole al’amuransu su zama daban-daban.
Wata rana na tambayi mai bai wa mataimakin shugaban kasar Nijeriya shawara a kan harkokin siyasa, Dr. Hakeem Baba Ahmed a ofishinsa na Jami’ar Baze dake Abuja (kafin a nada shi wannan mukamin) game da asalin tushen matsalar Nijeriya, ya ce “tsarin da Turawa suka zabar mana suka dora mu a kai.”
Ko a kwanan nan, wasu ’yan Nijeriya na ta kiraye-kirayen a yi watsi da tsarin dimokuradiyyar Amurka mai majalisun dokoki na kasa guda biyu, a soke majalisar dattawa, a bar ta wakilai kadai saboda dimbin makudan kudin da ake kashe musu alhali kuma tattalin arzikin kasar yana cikin wani hali.
Tun a shekaru aru-aru, Amurka ke shirya kisisina a sassan duniya da sunan yada tsarinta na dimokuradiyya wadda hatta wasu Amurkawa masu son gaskiya suna tofin Allah-tsine a kai.
A wata mukala da aka wallafa a shafin intanet na Cibiyar Nazarin Manufofin Harkokin Waje a 2023 mai taken “Daukaka Dimokuradiyya Bayan Yakin Iraki), babbar jami’a a Cibiyar Nazarin Manufofin Harkokin Waje a Gabas ta Tsakiya, Mai neman zama Farfesar Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Pennsylvania, kuma Ma’aikaciyar Bincike a Cibiyar Nazarin Kasa da Kasa ta MacMillan, Sarah Bush, ta ce, “Dimokuradiyyar Amurka tana da aibi da yawa. Na farko, akwai munafunci. Bayan haka, Amurka ta yi nesa daga bin cikakkiyar dimokuradiyya ita kanta. Amincewar da aka yi mata a matsayin mai kare martabar dimokiradiyya a duniya ta lalace. Na biyu, bai dace Amurka ta ce ta damu da dimokuradiyya ba alhali tana da alaka da wasu shugabannin danniya mafi muni a duniya.”
Ke nan yanzu ita kanta Amurka tana bukatar gyara, da girmama zabin kasashen duniya na salon dimokuradiyyarsu ba tilasta bin tsarinta mai kama da “kura da fatar kare” ba, da ke yamutsa hazo a duniya.
Duniya ta shaida husumar da Amurka ta haddasa a kasashen Larabawa da sunan yada dimokuradiyyarta musamman a 2011. Malamin kimiyyar siyasa a Jami’ar Port da kuma Jami’ar British da ke Masar, Gamal M. Selim ya ruwaito a mukalarsa mai taken “The United States And The Arab Spring: The Dynamics Of Political Engineering” daga Mark Glenn na Kungiyar Fafutukar Dimokuradiyya ta “Crescent and Cross Solidarity Movement” cewa, “Boren kasashen Larabawa wani sakamako ne na kokarin da Amurka ta yi tun daga shekara ta 2008 na kawar da wasu gwamnatocin kasashen Larabawa ta hanyar kafa dimokuradiyya da gwamnatin Amurka ke daukar nauyinta.”
Kowa ya ga yadda abin da Amurka ta yi ya jaza bala’i a Libiya da Iraki da Afghanistan da kuma goyon bayan murkushe zaben farko da aka yi cikin ‘yanci a Masar a 2013. Sannan uwa uba, zamanta kanwa uwar-gamin hana Falasdinawa ‘yanci duk da kisan kare dangi da ake musu tun daga 1948 har zuwa yanzu.
Dimokuradiyya ta asali dai ko tawane tsari aka bi, ita ce wacce ta bai wa al’umma zabi suka samar wa kansu mafita a kan komai ba tare da shiga-sharo-ba-shanun wasu bakin-haure ba!