Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) ta rushe babban taron jam’iyyar LP na kasa da ya gudana a Nnewi cikin Jihar Anambra.
Babban sakataren yada labarai na shugaban INEC, Mista Rotimi Oyekanmi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja.
- Gwamna Fintiri Ya Maka Dakataccen Kwamishinan INEC Na Adamawa, Hudu Ari A Kotu
- Yadda Musulmi Ke Shirye-shiryen Bikin Karamar Sallah Cikin Tsadar Rayuwa
Oyekanmi ya ce babban taron jam’iyyar LP na kasa bai samu sa idon jami’an INEC ba, sai dai bai bayyana dalilan da suka saka hukumar ba ta sa ido a babban taron ba.
NAN ya ruwaito cewa a ranar Talata da ta gabata ce jam’iyyar LP ta sauya wurin gudanar da babban taron nata daga Umuahia zuwa Nnewi.
Da yake bayani kan sauya wurin taron, babban lauyan LP, Mista Kehinde Edun ya bayyana wa manema labarai cewa jam’iyyar ta sanar wa INEC kan sauyin wuri da kuma ranar taron.
“Babban taronmu ya gudana ne a Nnewi da ke Jihar Anambra, ba a Umuahia na Jihar Abiya ba. Da farko mun tsara za mu gudanar da taron ne a Umuahia, inda daga baya muka sauya zuwa Nnewi.
“Muna da daman zabar duk wurin da muke so mu gudanar da taronmu. Abin da akwai ake bukata shi ne mu sanar wa INEC kan canji wuri da lokaci,” in ji Edun.
Sashi na 82 (1) na dokar zaben shekara 2022 ya bayyana cewa dole ne jam’iyyun siyasa su sanai wa Hukumar INEC idan za su yi babban taro na kasa ko wani taro akalla kwanaki 21 kafin taron.
Wannan ya hada har da taron ko ganawa na zaben mambobin kwamitin zartarwa da kuma sauran kwamitoci ko zaben ‘yan takara.