Hadimai da makusantan fitaccen Shehin malamin darikar Tijjaniyya a Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun karyata jita-jitan da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa, Shehin Malamin ya rasu.
Hadiman sun misalta labarin a matsayin kanzon kurege wanda bai da tushe balle makama kwata-kwata.
- Zargin Zagon Kasa Kan Ciyarwa A Watan Ramadan: Gwamnan Jigawa Ya Dakatar Da Kwamishinan Kasuwanci
- Wadanda Suka Wawashe Hatsi A Kebbi Sun Shiga Firgici Bayan Kwace Buhun Shinkafa 2,000
Idan za a tuna dai tun a makon jiya ne aka yi ta yada labarin cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi na fama da jinyar rashin lafiya mai tsanani, lamarin da ma makusantansa suka karyata. Sai kuma a ‘yan kwanakin nan masu yada jita-jitan suka canza salo zuwa cewa ya ma rasu.
Da ya ke zantawa da wakilinmu Malam Daha Azhary Bauchi wanda hadimi ne na kusa ga Sheikh Dahiru, ya ce, “Maulana Shehi yana cikin koshin lafiya. Yau ma zai dawo Bauchi daga Abuja. Yau da yamma zai dawo Bauchi.”
“Wasu ne kawai ke samun wuri su shirya karya su yada domin tayar wa jama’a da hankali. Amma lallai labarin karya ne,” ya shaida.
Kazalika, wani Hadimin babban malamin, Malam Garba shi ma ya karyata labarin da ake yadawa, “Shehi na nan da ransa. Zai dawo Bauchi a ranar Asabar saboda an rufe tafsir. Zai dawo Bauchi ne saboda a bana ba zai je Umra a kasa mai tsarki kamar yadda ya saba ba.
“Yana nan lafiya illa kawai yanayin jiki irin ta tsufa. Muna adduar Allah kara wa Shehi lafiya da nisan kwana. Su kuma masu yada jita-jitan muna addu’ar Allah shiryesu.”
Daya daga cikin ‘ya’yan Sheikh Dahiru Bauchi, Sirr Abdallah Sheikh ya wallafa shafinsa na Facebook a ranar Asabar dauke da sabbin hotunan shehin inda yake taya mahaifinsa murnar kammala tafsirin alkur’ani na bana.
Abdallah wallafa da cewa, “Alhamdulillah muna taya maulana Sheikh murnar kammala tafsirin bana 2024 lafiya, da fatan Allah ya kara lafiya ya nuna mana na shekara mai zuwa. Shehu mungode!.”
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake yada irin wannan jita-jitan ba, domin kuwa a lokuta mabanbanta an yada cewa Sheikh Dahiru ya rasu ya fi sau goma.