Bishiyar Dogon-yaro na fara fitar da ‘ya’ya ne daga shekaru uku zuwa biyar, inda kuma ta ke kammala girma a cikin tsawon shekaru goma.
A duk shekara bishiyar na samar da ya’ya’ da yawansu ya kai kimanin kilogiram 50, haka zalika; bishiyar na shafe dimbin shekaru a duniya ba tare da komai ya same ta ba.
- Sin Na Goyon Bayan Yunkurin IAEA Na Tabbatar Da Tsaron Tashar Nukiliya Ta Zaporizhzhia
- Ana Gudanar Da Horo Kan Gina “Koren Babbar Ganuwa” A Afirka A Beijing
Zuwa Tsawon Wane Lokaci Irin Dogon-yaro Ke Kammala Girma?
Irin Dogon-yaro na da gajeriyar rayuwa; ba ya yin tsawon kwana, domin kuwa yana kai wa daga kwana 10 ne zuwa 12 a lokacin da yake a danyensa. Don haka, ana so ka tabbatar da ka samu ingantaccen Irin da zai yi saurin nuna bayan shuka shi.
Haka zalika, ana so a tabbatar an rufe shi a cikin Tukunya; domin ya kasance ya na samu lema, wanda hakan kan taimaka masa daukar tsawon kwanaki ko mako uku, bayan shuka shi.
Wacce Kasa Ce Aka Fi Samun Bishiyar Dogon Yaro?
A bisa rahotannin masana a kan harkokin kimiyya da fasaha da kuma binciken da cibiyar bunkasa aikin noma ta kasa da kasa suka gudanar a shekarar 1992 sun bayyana cewa, an fi shuka bishiyar Dogon-yaro a bangaren Asiya da Nahiyar Afirka da kuma wasu kasahe na fadin duniya.
Har wa yau, kusan kashi 60 cikin 100 na al’ummar da ke Kasar Indiya; na shuka wannan bishiya ta Dogon-yaro.
Wace Irin Kasar Noma Bishiyar Dogon-yaro Ta Fi Bukata?
Bishiyar Dogon-yaro ta fi bukatar kasar noma mai inganci, sannan kuma ba a so a shuka Irin a wajen da ruwa ya ke yawan zama.
Wane Bangare Na Bishiyar Dogon-yaro Ne Ake Amfai Da Shi Wajen Sarrafa Magunguna?
Baya ga ita bishiyar ta Dogon-yaro, ana kuma amfani da ganyenta da Irinta da kuma jikinta wajen sarrafa magungunan gargajiya.
Yaya Ake Adana Ganyen Bishiyar Dogon-yaro Ya Dauki Tsawon Lokaci?
Da farko dai, za ka ciro wannan ganye daga jikin wannan bishiya ta Dogon-yaro.
Sannan, matali na biyu kuma ana so ka zuba ganyen a cikin kwano, sai ka rufe shi domin ya tsotse Lemar da ke jikinsa; sannan kuma sai ka rufe shi.
Mataki na uku kuma shi ne, saka shi a cikin firji ko na’ura mai sanyi.
Yadda Ake Tatsar Man Dogon-yaro Daga Ganyensa
Ana bukatar a nika shi, sannan sai a dora shi a kan wuta a tafasa shi ya dauki kamar minti 15, bayan ka sauke shi daga wutar sai ka bar shi ya yi kamar awa biyu ko sama da haka.
Daga nan, sai ka adana shi a wurin da yake a bushe; kana kuma ka tabbatar da cewa, rana ba ta kai ga inda yake ba.
Ana Samun Dimbin Kudaden Shiga A Noman Bishiyar Dogon-yaro
A yanzu haka, bishiyar Dogon-yaro na kara samun karbuwa a fadin duniya, musamman ganin yadda fannin ke samar da kudaden shiga masu daman gaske, haka nan kuma akwai masa’antu da ke sayen sa; domin sarrfaa shi zuwa wasu nau’ikan abubuwa da dama kamar: magunguna, man shafawa da sauran makamantansu.
Har ila yau, bishiyar Dogon-yaro na jurewa fari; sannan kuma bishiyar ta fi son yanayin da bai wuce 21°C zuwa 32°C ko kuma 70°F ko 90°F.
Bugu da kari, wani kwararre a fannin wannan noma na bishiyar Dogon-yaro, Dakta Abdullahi Ahmed Yar’adua ya bayyana cewa, lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali wajen bunkasa noman Dogon-yaro fiye da yadda Kasar Indiya ke yi a halin yanzu.
Dr Yar’adua ya tabbatar da cewa, Indiya na da kimanin bishiyar Dogon-yaro da suka kai kimanin miliyan 20, inda ya kara da cewa; daga shekarar 1985 zuwa 1995, gwamnatin kasar na samun kudaden shiga da suka tasamma kimanin dala biliyan 2.5 daga man da take samu daga wannan bishiya ta Dogon-yaro.
Sannan ya sanar da cewa, ana sarrafa ganyen wannan bishiya wajen sarrafa takin zamani, inda ya dora laifin yadda fanin ke samun koma baya a kan yadda shugabanin kasar nan ko kadan ba sa mayar da hankali kan noman Dogon-yaro.
Haka zalika, ya kuma koka a kan yadda aka yi watsi da masa’antar noman Dogon-yaro, wadda tsohuwar gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo ya kafa a Jihar Katsina.
Dr Yar’adua ya kuma shawarci gwamnati ta mayar da hankali wajen noman bishiyar Dogon-yaro, musamman ganin yadda ake samun kudaden shiga masu masu dimbin yawa a sauran kasashen duniya daban-daban.