Hukumar kula da bayar da bashin dalibai ta Nijeriya (NELFUND), karkashin jagorancin, Mista Akintunde Sawyerr, ta sanar da ranar 24 ga watan Mayu, 2024, a matsayin ranar da za a bude shafin bayar da bashin dalibai.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar da yammacin Alhamis.
- Sin: Karbuwar Hajojin Sin Masu Nasaba Da Sabbin Makamashi Ba Shi Da Nasaba Da Samar Da Tallafi
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Sun Sace 130 A Zamfara
Sanarwar ta ce an samu ci gaban ne bayan jajircewa da Shugaba Bola Tinubu ya yi na ganin daliban Nijeriya sun samu ilimi cikin sauki.
“Ta hanyar ahafin, dalibai za su iya neman bashi don ci gaba da karatunsu ba tare da matsalar kudi ba.
“Shafin ma Intanet zai bai wa dalibai dama cikin sauki domin neman bashi game da iliminsu.
“Muna karfafa wa dukkan daliban da suka cancanta da su yi amfani da wannan dama domin inganta makomarsu” a cewar Ayitogo.
A cewarsa dalibai za su iya ziyartar wannan shafin www.nelf.gov.ng domin neman bashin da za su habaka iliminsu.