Jami’an rundunar ‘yansanda a Jihar Imo sun kama wata mata ‘yar shekara 27 mai suna Oluchi Nzemechi bisa zarginta da daba wa saurayinta, Kelechi Nzemechi, wuka har lahira sakamakon wata rigima da ta kaure tsakaninsu a kan kin ba ta kasonta na kudin da suka yi damfara ta intanet.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yansandan Jihar, Henry Okoye, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Owerri a lokacin da yake gabatar da wacce ake zargin, ya ce Oluchi ta amsa laifin kashe saurayin nata ne kan kin ba ta kaso daga sama da kudin kasar Indonesiya miliyan 250 da suka damfari wani mutum dan kasar.
- Dan Takarar Gwamnan Katsina A NNPP Ya Ba Da Tallafin Miliyan 50 Ga ‘Yan Gudun Hijira
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
Da take bayar da labarin mummunan al’amarin, rundunar ‘yansandan ta bayyana cewa wacce ake zargin ta yi ikirarin cewa saurayin nata da ta kashe ya gabatar da ita ga wanda za su damfara har ta kai ga sun samu wadannan kudade, inda ta kara da cewa ta yi amfani da wuka a kicin wajen daba masa wuka bayan da suka yi zazzafar gardama.
“Rundunar ‘yansandan ta gudanar da bincike mai zurfi sun cafke wata budurwa ‘yar shekara 27 mai suna Oluchi Nzemechi da ke unguwar Uzoagba a Karamar Hukumar Ikeduru ta Jihar Imo da laifin daba wa abokin aikinta, Kelechi Nzemechi, mai shekaru 31 wuka wanda ya kai shi ga mutuwa.
“Yayin da take amsa tambaya, wacce ake zargin ta amsa laifinta, ta yarda cewa masoyinta ne ya yaudare ta inda ya jefa hanyar damfarar intanet mai suna ‘yahoo yahoo’.
A ranar 02/06/2024, ta yi zazzafar husuma da shi saboda ya kasa ba ta wani kaso na kudin da ake zargin ta kai Rupiah Miliyan 250 da suka samu daga hannun wani da suka damfara a Indonesia, inda daga nan ne ta yi amfani da wukar kicin ta daba masa wuka a wani bangare na jikinsa,” in ji ‘yan sanda.
A lokacin da take zantawa da ‘yan jarida, Oluchi ta bayyana yadda ta yi kokarin wanke kanta daga kashe shi ta hanyar rubuta wasikar yaudara, “A kokarin da na ke na boye laifina, na yi gaggawar rubutawa a takarda; ‘Kana tunanin za ka ci kudina ka tafi haka, ni uwa ce ga samari, ina zuwa don neman matarka da yaronka har da danginka. Sai na dora takardar a kan gawar sannan na gudu daga gidan,” in ji ta.
Wacce ake zargin ta kuma bayyana cewa tana zaune da wanda ta kashe tun shekarar 2019 inda suka haifi yaro tare. ASP Okoye ya ce za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.