Babban Sufeton ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, Ph.D., NPM, ya yi wa al’umma jawabi dangane da shirye-shiryen zanga-zangar ƙasa baki ɗaya, yana mai jaddada mummunan tasirin da zanga-zanga mai tashin hankali zai iya yi wa al’umma. A cikin jawabin nasa, IGP ya bayyana muhimman batutuwan da ke nuna muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a yayin zanga-zanga.
“Ba a Nijeriya kadai ake fama da wahala ba. Wannan bala’i ne na duniya. Shin gwamnati tana yin wani abu game da shi? Eh! Wannan shi ne abin da gwamnati mai sauraren jama’a ke yi,” in ji IGP. Ya jaddada cewa matsin da ƙalubalen tattalin arziki na yanzu ba a iya Nijeriya ne kaɗai ba kuma gwamnati na aiki tukuru don rage tasirin su da kuma samar da sauƙi ga ‘yan ƙasa.
- ‘Yan Nijeriya Na Da Hakki Su Yi Zanga-zangar Lumana, In Ji Fadar Shugaban Kasa
- Hukunce-Hukuncen Sallar Idi Da Zakatul Fidir
Yayin da yake tuna abin da ya faru a zanga-zangar EndSARS na shekarar 2020, IGP ya ce, “Lokacin da aka ƙona ofisoshin ‘yan sanda, makamai da yawa sun shiga hannun miyagun mutane.
“Akwai isassun darussa da za a koya daga zanga-zangar tashin hankali a baya a Nijeriya,” in ji IGP, yana kira ga ‘yan ƙasa da su tuna da rikici da wahalar da suka biyo bayan irin wadannan abubuwan. “Babban haɗari na zuwa da zanga-zangar da ba a yi ta cikin lumana ba, ya ƙara da jaddada yiwuwar rasa rayuka, da lalata dukiyoyi, da kuma fargaba cikin al’umma.
IGP ya amince da haƙƙinsa yin zanga-zanga, yana cewa, “ƴan ƙasa na da haƙƙin yin zanga-zanga ne amma ta lumana.” Ya kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan hakki cikin kishin ƙasa, su kuma kauce wa ayyukan da za su iya rikiɗewa zuwa tashin hankali.