Majalisar Dattawa ta koka kan asarar sama da Naira biliyan daya da manoman Citta a Kudancin Kaduna suka tabka, biyo bayan bulla cutar da ta lalata gonakin manoma da dama a fadinn yankin.
Sakamakon wannan asara ne ya sa majalisar ta bukaci hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), da ta taimaka wa manoman da abin ya shafa da kayan agaji.
- Tura Ta Kai Bango, Zanga-zanga Ta Kai Gidan Buhari Da Sarkin Daura
- Wang Yi Ya Jaddada Muhimmancin Diflomasiyya Tsakanin Mabanbantan Al’ummu
Kazalika, majalisar ta kuma umarci ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci da kuma hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC), da su garzaya yankin; domin magance cutar cikin gaggawa.
Wannan umarni na majalisar dai, ya biyo bayan kudurin da Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu, Marshall Katung ya gabatar ga zauren majalisa ta kasa, inda ya yi kira da a dakile ci gaba da yaduwar cutar a gonakin manoman yankin.
Sanata Babangida Hussaini daga Jigawa, Titus Zam daga Biniwe da kuma Kelbin Chukwu daga Enugu ta Gabas ne suka goyi bayan kundurin na Sanata Mashal.
Katung ya ce, tun a shekarar 1927 ake yin noman Citta a wannan yankin, sannan Cittar da ake nomawa a yankin ita ce kan gaba a dukkanin fadin kasar nan, inda kuma hakan ya sa ake samar da yawan wadda ake samu a duniya baki-daya.
A cewar sa, a kalla an noma sama da tan 300,000 na Citta daga t 2014 zuwa 2018, wadda a kasuwar duniya ta kai kimain kashi 11 a cikin dari, inda kasar Indiya ce kawai, ke a kan gaba.
Har ila yau kuma, ya koka kan bullar cutar a shekarar 2023; a kananan hukumomi bakwai, wadda ta yi sanadiyyar lalata sama da hekta 2,500, wanda aka kiyasta asarar ta kai ta Naira biliyan 10, da hakan ya zamo wata barazana da ta shafi karancin nomanta a duniya baki-daya.