• English
  • Business News
Saturday, August 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro: Bukatar Daukar Kwakkwaran Mataki

by Leadership Hausa and Sulaiman
11 months ago
in Labarai
0
tsaro
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Nijeriya ta sake samun kanta a cikin halin tashin hankali, tsoro da alhini, a yayin da rahotanni suke nuna cewa, ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da daruruwan dalibai ‘yan makaranta a wasu jihohin kasar nan, hakan shi ya dawo da hannun agogo baya a kokarin da ake yi na samar da tsaro a kasar nan.

A kwanaki ne ‘yan ta’adda suka sace dalibai 280 da malaman su daga makarantar LEA da ke garin Kuriga, ta Jihar Kaduna.

  • Shugabannin Tsaro Sun Gaza, Ya Kamata Gwamnati Ta Sake Lale – Farfesa Lugga
  • Karin Harajin Amurka Ba Zai Dakile Sashen Kere-Keren Kasar Sin Ba

Hakanan ma wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari yankin Buda da ke karamar hukumar Kajuru duk dai a Jihar Kaduna inda suka yi nasarar sace mutum 61.

Duk a ‘yan kwanakin nan, sai gashi kuma ‘yan ta’addar Boko Haram sun yi awon gaba da mata 200 a yankin Gamboru-Ngala da kuma karamar hukumar Dikwa a Jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa, matan da aka sace na daga cikin ‘yan gudun hijira da ayyukan ta’addanci ya raba su da muhallansu, an kuma sace su ne a yayin da suka shiga daji don neman itacen dafa abinci.
Bugu da kari mun samu rahoton kashe mutum 50 ciki har da iyalai 7 a harin da ‘yan ta’adda suka kai yankin Gbagir da ke karamar hukumar Ukum ta Jihar Benuwai.

Labarai Masu Nasaba

Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Taimaka Wa Ballewar Daurarru A Gidan Yari

UNICEF Na Neman Naira Biliyan 240 Don Ayyukan Agaji A Nijeriya

A daidai lokacin ne da ‘yan ta’addan ke ci gaba cin karensu babu babbaka sai kuma gashi sun kai hari kauyen Gidan Bakuso da ke karamar hukumar Gada a Jihar Sakkwato, sun kuma yi awon gaba da almajirai ‘yan tsangaya 15 wadanda kuma da dama ba a samu labarinsu ba zuwa yanzu.

A ra’ayin wannan jaridar wadannan ayyuykan ta’addanci ba abin da ya kamata a sa ido ana kallo ba ne; wadannan sun kasance wasu sabbin babi ne a cikin ayyukan ta’addanci da ya addabi sassan Nijeriya a cikin ‘yan shekarun da suka gabata.

Nijeriya ta dade tana dandana kudarta cikin ayyyukan ‘yan ta’adda da ke harkokinsu ba tare da wani tsoro ba a sassan Nijeriya.

Wadannan ayyukan garkuwa da mutane da suka sake kunno kai sun yi matukar tayar da hankulan al’umma, wadanda suka dade suna sauraron alkawuran da aka yi wa ‘yan kasa cewa, lallai za a samar masu da tsaro amma kuma har yanzu babu ranar tabbatar da wancan alkawarin.

A ra’ayinmu, lokaci ya yi da za a canza salon da ake amfani da shi a yaki da ta’addanci a Nijeriya. Duk da cewa, gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta gaji wasu daga cikin matsalolin tsaron da ake fuskanta, matsalar da take barazana da kokarin jawo masu zuba jari da kuma huldar Nijeriya da kasashen waje.

A ra’ayinmu, duk irin abubuwan da ya shirya gabatarwa na ci gaban kasa, lamarin samar da tsaro shi ya kamata ya zama a sahun gaba don da shi ne tarihi zai kalli yadda ya tafiyar da al’ummar kasa, musamman ma ganin yadda ake kashe mutane ba tare da kakkautawa ba.

Matsayar shugaban kasa ta kin biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda abin a yaba ne, hakan ya yi daidai da yadda ake tafiyar da irin wannan matsalar a sassan duniya yana kuma aikawa da sako mai karfi ga ‘yan ta’addan da ‘yan bindiga cewa, gwamnati a shirye take ta murkushe su.

Amma kuma dole gwamnati ta fito da tsari na musamman na yadda za ta karya alkadarin ‘yan ta’addan ba tare da wani bata lokaci ba.

Tattaunawa da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan Bindiga baya haifar da da mai ido, irin tattauanwar tana kara karfafa kungiyoyin ne kawai yana kuma nuna tamkar gwamnati bata da yadda za ta yi ba.
Muna kara jaddada cewa, bai kamata Nijeriya ta nuna gazawa ba a fafatawarta da ‘yan ta’addan da suka gallazawa al’umma ba tare da tausayi ba. Lokacin duk wani tattuanawsa ya wuce, abin da ake bukata a halin yanzu shi ne fafatawa da gungun masu aikata laifi.

Domin samun wannan nasarar, dole ne Shugaba Tinubu ya karfafawa jami’an tsaronmu ta hanyar samar masu da dukkan kayan aiki na zamani daidai da irin wadanda ake amfani da su a kasashen duniya da suka ci gaba. Haka kuma a kwai bukatar a karfafa hanyoyin samar da bayanan sirri don dakile ayyukan ‘yan ta’adda a daidai lokacin da suke shirya ayyukan su.

Har ila yau ya kamata a yi maganin ainihin matsalolin da suke taimakawa wajen bunkasar harkokin ta’addanci a Nijeriya wadanda suka hada da talauci, rashin aikin yi ga matanasu da kuma yadda ake nunawa wasu al’umma wariya a harkokin yau da kullum na kasa.

Ya kamata a samar da ingantaccen tsarin yaki da ta’addanci wanda kuma ya hada da samar da ayyukan bunkasa rayuwar al’umma da suka hada da samar da aikin yi ga matasa, bunkasa bangaren ilimi, kiwon lafiya, da kuma sauraron koke koken al’umma.

Nijeriya kasa ce da ke da al’umma masu aiki tukuru, mun sha fuskantar matsaloli mun kuma yi maganinsu cikin dan kankanin lokaci. Yanzu lokaci ya yi da dukkan dan Nijeriya zai bayar da tasa gundumawar don ganin an kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ba tare da nuna bambancin siyasa, kabilanci ko addini ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Zamfara: Yadda Zargin Juna Da Hannu A Ta’addanci Ya Yi Kamari Tsakanin Dauda Da Matawalle

Next Post

Mahangar Masana Kan Yawaitar Ibtila’i A Arewa

Related

Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Taimaka Wa Ballewar Daurarru A Gidan Yari
Rahotonni

Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Taimaka Wa Ballewar Daurarru A Gidan Yari

57 minutes ago
UNICEF Na Neman Naira Biliyan 240 Don Ayyukan Agaji A Nijeriya
Labarai

UNICEF Na Neman Naira Biliyan 240 Don Ayyukan Agaji A Nijeriya

10 hours ago
Ɓarayin Waya Sun Hallaka Ɗalibin ATAP A Bauchi
Labarai

Ɓarayin Waya Sun Hallaka Ɗalibin ATAP A Bauchi

11 hours ago
JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa
Labarai

JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa

11 hours ago
Raguwar Hauhawar Farashi: ‘Yan Nijeriya Da ‘Yan Kasuwa Ba Su Ga Saukin A Zahirance Ba
Labarai

Raguwar Hauhawar Farashi: ‘Yan Nijeriya Da ‘Yan Kasuwa Ba Su Ga Saukin A Zahirance Ba

12 hours ago
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Jagororin ‘Yan Bindiga A Abuja, Sun Ƙwato Makamai Da ₦7.4m

14 hours ago
Next Post
Mahangar Masana Kan Yawaitar Ibtila’i A Arewa

Mahangar Masana Kan Yawaitar Ibtila'i A Arewa

LABARAI MASU NASABA

Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Taimaka Wa Ballewar Daurarru A Gidan Yari

Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Taimaka Wa Ballewar Daurarru A Gidan Yari

August 23, 2025
Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama

Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama

August 22, 2025
UNICEF Na Neman Naira Biliyan 240 Don Ayyukan Agaji A Nijeriya

UNICEF Na Neman Naira Biliyan 240 Don Ayyukan Agaji A Nijeriya

August 22, 2025
Sin Ta Samu Karin Kamfanoni Kusan Miliyan 20 A Cikin Shirin Shekaru Biyar Karo Na 14

Sin Ta Samu Karin Kamfanoni Kusan Miliyan 20 A Cikin Shirin Shekaru Biyar Karo Na 14

August 22, 2025
Ɓarayin Waya Sun Hallaka Ɗalibin ATAP A Bauchi

Ɓarayin Waya Sun Hallaka Ɗalibin ATAP A Bauchi

August 22, 2025
JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa

JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa

August 22, 2025
Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12

Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12

August 22, 2025
Raguwar Hauhawar Farashi: ‘Yan Nijeriya Da ‘Yan Kasuwa Ba Su Ga Saukin A Zahirance Ba

Raguwar Hauhawar Farashi: ‘Yan Nijeriya Da ‘Yan Kasuwa Ba Su Ga Saukin A Zahirance Ba

August 22, 2025
Kamfanin Novo Nordisk Na Denmark Zai Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar Sin A Bana

Kamfanin Novo Nordisk Na Denmark Zai Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar Sin A Bana

August 22, 2025
Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin SCO Na 2025

Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin SCO Na 2025

August 22, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.