Ma’aikaci mutum ne da aka dauke shi domin hidimta wa jama’a a cikin ayyuka irin na gwamnati, kodayake ma’aikacin yana kasuwa zuwa kashi biyu, akwai ma’aikaci mai kula da kirkiro ayyuka da sa idon ganin ana aiwatar da ayyukan, akwai kuma mai hidimta wa jama’a kai-tsaye. Kodayake duka biyun danjuma ne dai da danjummai.
Galibin ma’aikatan gwamnati masu hidimta wa jama’a kai-tsaye suna fara aiki ne a matsayin ma’aikatan da ke kula da tsare-tsare saboda ka’idojin aikin gwamnati, ban taba jin ko akwai ka’idojin aikinsu daban ba, amma kuma ina da masaniya a kan ka’idojin aikin wadanda ke hidimta wa jama’a kai-tsaye. Sun hada da dokokin daukar aiki, karin girma da ladabtarwa da ake amfani da su a kan kowane ma’aikaci. Kodayke sojoji, jami’an tsaro da sauran wasu hukumomi sun zame suka kafa nasu dokokin amma ga kowane ma’aikaci mai hidimta wa jama’a, baya ga tsarin mulki ba shi da wata doka sai ta tsarin aikin gwamnati.
- Gwamnati Ba Za Ta Ci Gaba Da Biyan Tallafin Aikin Hajji Ba – NAHCON
- Nazari A Kan Tsare-tsaren Aikin Noma Na Nijeriya Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai
Saboda haka wane ne ma’aikacin gwamnati mai hidimta wa jama’a, wanda ake nadawa ya yi aiki a cikin harkokin gwamnati tsundum kamar irin su ministoci, jakadoji, manajan daraktoci, manyan shugabannin hukumomin gwamnati, manyan daraktoci, mambobin hukumomin sojoji da jami’an tsaro da sauransu, dukkansu ana daukarsu a matsayin masu hidimta wa jama’a ne duk da cewa akwai bambanci a bangarorin da suke yin aiki.
Da zarar mutane sun fahimci wannan, to za su zage damtse wajen zama ma’aikatan gwamnati masu hidimta wa jama’a amma ba hidimta wa kansu ba. Abin da ya fi bata lamurra a yau a cikin al’ummarmu shi ne samun ma’aikatan gwamnati masu hidima ga jama’a da ba su cancanta ba kamar yadda aka ambata a littafin da tsohon Ministan Abuja kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya rubuta.
Mutum ne sahihi mai kaifin basira, yana cikin sahun su Sule Lamido, Sarki Sanusi Lamido Sanusi, tsohon Gwamnan CBN kuma Sarkin Kano, Dr. Akinwumi Adesina, Shugaban Bankin Raya Afirka, Dr. Oby Ezekwesili, Charles Soludo, Peter Obi, Dr. Obadiah Mailafiya, Farfesa Ango Abdullahi, dukkan wadannan mutane ne masu kaifin basira da suka yi shuhura. Kuma su ne ma’aikatan gwamnati da suka hidimta wa jama’a a bisa mizanina.
Idan aka duba batun da muke magana a kai na “Ma’aikacin Gwamnati Da Ya Tsinci Kansa A Aiki”, batu ne musamman na tafka muhawara a kai, yana da ma’ana daban-daban. Misali, a wurin Malam Nasiru El-Rufa’i, hakan na nufin mutane ko mutumin da ya tsinci kansa a wani mukami da bai shirya masa ba, a wurin wasu kuma, abin ya sha bamban.
Amma me ya sa? Idan aka nada mutum a wani mukami da ba shi da cikakkiyar masaniya ko kuma bai ma san aikin da aka ba shi ba kwata-kwata, to idan yana so ya nuna kishin kasa da hali nagari, sai ya ki karba, ko ya yi murabus domin bai wa wadanda suka cancanta masu kwarewa sarari su taimaka wajen ciyar da kasa gaba.
Amma shi wanda ya zama ma’aikaci bisa kaddara ba don cancanta ba, ba zai taba yin haka ba kuma ba zai nemi ilimin wannan aiki da aka ba shi ba don samun nasara. Irin su ne za ka ga suna wa mutane kamar sun fi kowa ilimi. Sai su rika zalunci da kama-karya wajen gudanar da ofisoshinsu. Maimakon su jawo kwararru da suka san aiki sai su shamakance su. Ta haka za su rika kunyata wadanda suka nada su har ta kai ga an wayi gari an kore su, duk kunya ta lullube su saboda gazawarsu. Irin wadannan ma’aikata bata gari ne a cikin gwamnati, ba su da kima da daraja, ga kauyanci da kuma yadda suke kasancewa kadangaren bakin tulu, ka ki shiga, ka ki fita.
Irin wadannan ma’aikata marasa cancanta sun fi yawa a ofisoshin gwamnati saboda ba su da gurbi a kamfanoni masu zaman kansu ko kuma kamfanonin da ke neman riba. Nan da nan ake gane su a fatattake su, shi ya sa suke zuwa su fake a ma’aikatun gwamnati saboda an kawo su ne don suna da uwa a gindn murhu da kuma sauran harkalla marasa kyau. Don haka matukar ana so kasa ta ci gaba, dole ne a rika duba cancanta da ilimi da kaifin basira. Muna da mutane a kasar nan wadanda sun yi shuhura da kwazo da kaifin basira a duniya kamar su Dr. Ngozi Okonjo- Iweala, Dr. Amina Mohammed, Dr. Oby Ezekwesili, Dr Akinwumi Adeshina, Dr. Shamshudeen Usman, Dr. Jelani Aliyu wadanda suke haskawa a duniya. Kenan da a ce za a kawo wadannan cikin tsarin shugabancinmu na siyasa a cikin gida, me za su zama? Wannan tambaya ce da ta cancanci a bai wa wanda ya amsa kyautar Naira Miliyan Daya. Kuma amsar mai sauki ce, ita ce: za su samar da sarari da kuma shimfida aiki na ci gaba kamar yadda yake a kasashen duniya tare da tabbatar da shugabanci nagari.
Ma’aikatan gwamnati marasa cancanta ba su komai illa wargaza tsari da ci gaba wadanda suke zama karfen-kafa masu hana ruwa gudu da bata ruwa ba don su sha ba. Tabbas matukar muna bukatar samun ci gaba, to dole ne mu samo sahihan ma’aikata da suka cancanta amma ba wadanda kaddara ce ta kawo su ba kawai!
Amb. Abraham James, daga Kamfanin Harkokin Sadarwa da Labarai na Hallbibe. Email: [email protected].