Ireti Heebah Kingibe
Ireti Heebah Kingibe, injiniya ce yanzu kuma ‘yar siyasa ce, da ta lashe zaben kujerar Sanata mai wakiltar Babban Birnin Tarayya (FCT) a Majalisar Dattawan Nijeriya ta 10.
An zabe ta a karkashin Jam’iyyar Labour a zaben ‘yan Majalisar Dattawa na 2023 kuma ita ce shugabar kwamitin majalisar dattawa kan harkokin mata. Kingibe ta fara aiki ne a matsayin injiniya mai kula da ingancin a Bradley Precast Concrete Inc a (1978-1979) sannan ta yi aiki da sashen zane-zanen sufuri na Minnesota har zuwa 1981.
Ta dawo Nijeriya don hidimar bautar kasa (NYSC) a 1981. Ta yi aiki a matsayin mai kula da ayyuka a sansanin sojojin saman Nijeriya da ke Ikeja, Legas. A shekarar 1982 ta shiga kamfanin ‘New Nigeria Construction Company’ da ke Kaduna a matsayin Injiniyar tsare-tsare kafin ta ci gaba da aikin tuntuba da kamfanin Belsam Limited a shekarar 1985. Daga 1990 zuwa 1994, ta kasance Injiniya na yankin Lodigiani Nigeria Limited, Legas, kuma yanzu ita ce mai ba da shawara sannan kuma babbar abokiyar hurda a Kelnic Associates a Abuja.
Siyasar Kingibe ya fara ne a shekarar 1990 a matsayin mai ba da shawara ga shugaban rusasshiyar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP). Ta tsaya takarar kujerar sanatan FCT a karkashin jam’iyyar ANPP a shekarar 2003, sannan ta koma jam’iyyar PDP a 2006. A 2014 ta koma APC, amma ta fice daga jam’iyyar a 2015 takarar Sanata.
A shekarar 2022, ta shiga jam’iyyar Labour, ta zama ‘yar takarar sanata a FCT a zaben 2023, kuma ta yi nasara. Kafin zaben, ta kaddamar da ainihin albashinta don gudanar da ayyukan samar da ababen more rayuwa a yankunan karkara a cikin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Dr. Lydia Umar
Dr. Lydia Umar Kwararriyar ce mai ilimi, ta kware wajen ci gaban al’umma , kuma mai fafutuka, wacce ta kware a fannin karatun (Social Studies). Ta kafa kungiyar wayar da kan jama’a ta Gender Awareness Trust (GAT) a jihar Kaduna a shekarar 2000, inda ta yi kokrin inganta daidaiton jinsi, kiwon lafiyar haihuwa, shigar mata a siyasance, da samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin addinai daban-daban.
Tare da gogewa sama da shekaru 30 a aikin koyarwa da ayyukan ci gaba, Dokta Umar ta kasance mai himma wajen tafiyar da rikice-rikice, sasantawa, da gina zaman lafiya a matsayin mai koyarwa, sannan kuma mai bincike, kuma mai gudanarwa ta hukumomin gwamnati daban-daban da abokan ci gaban kasa da kasa.
Ta rike mukamai da dama da suka hada da mai bai wa kungiyar mata ta Afirka ta yamma shawara kan samar da zaman lafiya a yankin, da mamba a kungiyar raya zaman lafiya ta Afirka ta yamma (WANEP), ta yi mataimakiyar shugabar kungiyar sake fasalin ‘yan sanda a Nijeriya.
Dr. Umar ta wakilci Nijeriya a kungiyar Mata, daman lafiya da tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kuma ta ba da gudummawa sosai ga shirye-shiryen zaman lafiya na yanki da na duniya.
Ayyukan da ta yi suna da yawa da suka hada da jagorantar kokarin bayar da shawarwari don amincewa da dokar hana cin zarafi (BAPP) a Jihar Kaduna a 2018 da kuma tuntubar ci gaba da tsare-tsare na hukumar zaman lafiya ta Kaduna.
Gudunmawar da Dakta Umar ta bayar wajen ’yancin mata da samar da zaman lafiya ya sanya ta zama jigo a fagen ci gaban gida da waje, an santa da jajircewarta na tabbatar da daidaiton jinsi da adalci a cikin al’umma.
Aisha Pamela Sadauki
Aisha Pamela Sadauki ta kasance Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin gwamnatin Soja Abubakar Tanko Ayuba. Ta rike mukamai da dama a cikin gwamnatin Jihar Kaduna, ciki har da kwamishiniyar ci gaban al’umma, matasa, da wasanni a 1988 da kwamishiniyar ilimi a 1989, kafin ta zama mataimakiyar gwamna daga 1990 zuwa 1992. gudummawar da ta bayar, ga jiha da kasa baki daya, Aisha Sadauki ta samu lambar yabo ta kasa (OON) a shekarar 2000.
Beni Butmak Lar
Beni Lar, gogeggiyar ‘yan siyasa ce, sannan kuma masaniya ce a shari’a, kuma ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar Langtang ta Arewa/Kudanci a Jihar Filato. Da farko an zabe ta a shekara ta 2007, tana yin wa’adi na biyar ne kuma ita ce shugabar kwamitin majalisar kan ‘yancin dan’Adam. Ita ce babbar ‘yar Solomon Lar, tsohon Gwamnan Jihar Filato, da Farfesa Mary Lar.
A duk tsawon aikinta na majalisa, Beni Lar ta kasance mai fafutukar kare hakkin mata, kare yara, da yancin dan’Adam. Ta yi yunkurin kare mutuncin cin zarafin yara, tallafawa shirye-shiryen yaki da fataucin mutane, da kafa hukumar kare yara da tilastawa yara ta kasa.
A shekara ta 2008, ta jagoranci kwamitin kula da harkokin mata na majalisar wakilai, kuma ta taka rawar gani wajen magance matsalolin da suka shafi jinsi, ciki har da bayar da shawarwarin shigar da mata cikin harkokin mulki da kuma kawar da nuna wariya ga mata.
Beni Lar ta yi addu’a kuma ta tofa albarkacin bakinta kan harkokin tsaro da ci gaban kasa. Ta jagoranci zanga-zangar nuna goyon bayanta ga kokarin da sojojin Nijeriya ke yi na ceto ‘yan matan makarantar Chibok da aka sace tare da yin kira da a inganta hanyoyin mota a mazabarta bayan hare-haren makiyaya. Ta ba da shawarar samar da wuraren kiwo ga fulani makiyaya tare da fafutukar samar da mafita mai dorewa ga Nijeriya a matsayinta na tsohuwar shugabar kwamitin kimiyya da fasaha ta majalisar.