Aled Sienaert, kwararren mai fashin baki a fannin tattalin arziki a bankin duniya, ya sanar da cewa, karin mafi karancin albashi na kwanan baya da aka yiwa kananan ma’aikata a kasar nan, kashi 4.1 na ‘yan Nijeriya kacal, za su amfana da karin.
Ya bayyana haka ne, a wajen kaddamar da rahoton bunksar tattalin arzikin Nijeriya (NDU) da aka gudanar a Abuja.
- Abin Da Ya Sa Ƙasashen Duniya Suka Gina Majalisar Ɗinkin Duniya – Sakatare Janar
- Super Eagles Ta Hauro Matsayi Na 36 A Jadawalin Duniya Na FIFA
Sienaert, ya kara da cewa, karin albashin mai yawn gaske, amma amfana da shi bai da wata yawan gaske, duba da cewa, zai kawai, amfani kananan ma’aikatan ne.
Ya ci gaba da cewa, karin mafi karancin albashin da gwamnatin tarayya ta yi, zai amfani wani dan bangare na kananan ma’aikata ne, wanda kashi 4.1 na kananan ma’aikatan ne kawai, karin zai shafa kai tsaye.
Sienaert ya yi nuni da cewa, yakar talauci, na bukatar kara fadada aikin yi, inda ya sanar da cewa, akwai kuma bukatar a samar da aikin da zai kara ci gaba da da inganta rayuwar jama’a.
A cewarsa, sabon rahoton na bankin duniya ya bayyana cewa, rashin aikin yi, ba wai wata dama ce, da ke kara haifar da talauci ba.
Ya sanar da cewa, domin an dauki mutum a aiki, ba wai wata damace, ta gujewa talauci ba.
Ya ci gaba da cewa, “Ayyukan ofis-ofis da dama, da ma’aikata keyi, ba wai suna kara samar masu da kudaden shiga ban, wanda kuma albashin da ake biyansu, ba zai rage masu talauci ba.”
Bugu da kari, rahoton ya sanar da cewa, kara kirkiro da wasu ayyukan abu ne mai mahimmanci.
A cewar, tsare-tsaren sun mayar da hankali ne, a kan albashin da ake biyan kanannan ma’aikata, kamar a masana’antu masu zaman kansu, sai dai, tsare-tsaren, sun tsallake kanannan ma’aikata.
Rahoton ya kara da cewa, akwai matukar wuya wanzar da tsaren na mafi karancin albashin, ya isa kai tsaye ga kananan ma’aikata, domin ba suna yi aki a kan tsarin biyan mafi karancin albashi bane.
Wannan tsarin ma, ya shafi ma’aikatan da ke yin aiki, a masa’antu masu zaman kansu.
Bugu da kari, rahoton ya yi gardi da cewa, biyan albashi mai yawa, zai iya zamowa wani babban nauyi ga fannin ma’aikatun gwamnati
Rahoton ya kuma nuna cewa, akwai bukatar a samar da tsare-tsaren daukar aiki, da ke bukatar a rage talauci.