A ƙoƙarinta na tabbatar ta bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara ɗora masana’antar Kannywood a kan saiti, hukumar tace fina-finai da Ɗab’i ta Jahar Kano ƙarƙashin jagorancin Alh Abba El-mustapha ta ɗauki wani mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai ba tare da cika ƙa’idar da doka ta tanadar musu ba, na kawo kowanne Fim gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al’umma inda ta dakatar da cigaba da haska wasu Manyan Fina-finai har guda 22.
Abba El-mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami’an hukumar tare da dogon nazari domin kawo ƙarshen ƙorafe-ƙorafen da yace hukumar ke yawan karɓa don ƙara inganta aiyukan hukumar tare da masana’antar Kannywood, sanarwar tace hukumar ba zata lamunci karan tsaye akan harkar Fim ba a jihar Kano ba.
- Me Ya Sa Fina-finai Masu dogon Zango A Masana’antar kannywood ke Zama Cin kwan Makauniya?
- Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage
Ya ƙara da cewa doka ce ta bawa hukumar damar tace duk wani Fim tare da lura da aiyukan yan masana’antar Kannywood matsawar suna da rijista da hukumar a ko ina suke, saboda haka ana shawartar masu ɗaukar nauyin waɗannan fina-finai da su tabbatar da sun bi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka waɗannan fina-finai a gidajen TV ko kafar intanet.
Haka kuma ana sanar da su cewa su miƙo fina-finansu ga hukumar domin tantance su tare da ba su shaidar inganci ta tacewa nan da sati ɗaya mai zuwa domin guje wa fushin doka.
Daga ƙarshe hukumar ta nemi haɗin kan dukkannin gidajen TV da hukumar da ke lura da kafafen yaɗa labarai ta Nijeriya wato NBC kan su cigaba da taimaka mata wajen samun nasarar abinda ta saka a gaba da cigaban Jihar Kano da masana’antar Kannywood.
jami’in yaɗa labaran hukumar Abdullahi Sani Suleiman ya bayyana fina-finan da aka dakatar kamar haka:
1. Dakin Amarya
2. Mashahuri
3. Gidan Sarauta
4. Wasiyya
5. Tawakkaltu
6. Mijina
7. Wani Zamani
8. Labarina
9. Mallaka
10. Kudin Ruwa
11. Boka Ko Malam
12. Wa yasan Gobe
13. Rana Dubu
14. Manyan Mata
15. Fatake
16. Gwarwashi
17. Jamilun Jiddan
18. Shahadar Nabila
19. Dadin Kowa
20. Tabarma
21. Kishiyata
22. Rigar Aro
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp