Jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta yarda Amurka ko wata ƙasa su yi mata ƙarfa-ƙarfa ba.
Ya ce idan Amurka ta kai musu hari, za su rama kuma za su nuna ƙarfinsu.
- Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin Sun Samar Da Sabuwar Hanyar Sufuri Ga Al’Ummun Kasashen Shiyyar Tsakiyar Asiya
- An Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 12, An Kwato Makamai A Katsina
Wannan magana tasa ta zo ne bayan da Isra’ila ta ce ta kai hari kan wurare kusan 40 a Iran, ciki har da masana’antun ƙera makamai.
Ita ma Iran ta mayar da martani da jiragen yaƙi marasa matuƙa zuwa Isra’ila.
A wani ɓangare, ƙasashen Rasha da Amurka na ƙoƙarin tattaunawa don ganin an kawo ƙarshen wannan rikici, kamar yadda wani mataimakin ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Ryabkov, ya faɗa.
Ayatollah ya yi gargaɗi cewa, idan Amurka ta shiga cikin rikicin kai-tsaye don taimaka wa Isra’ila, wannan zai jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin matsala babba.
Rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ya shafe kwanaki shida yanzu, inda mutane da dama suka mutu a ɓangarori biyun, baya ga asarar dukiyoyi da gine-gine.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp