Kungiyar Izala ta Nijeriya ta yi kira ga hukumomi da su gaggauta gudanar da binciken keke-da-keke don tabbatar da ganin sun hukunta duk masu hannu a kisan gillar da aka yi wa fitaccen malamin nan na Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.
An kashe malamin ne a ranar Juma’a, inda rundunar ‘yan sandan jihar, ta tabbatar da cewa wasu sojoji biyu ake zargi da kisansa.
- Ba Ku Da Dalilin Ci Gaba Da Yajin Aiki – Badaru GA ASUU
- Mai Mala Buni Ya Bai Wa ‘Ya’yan Sheikh Aisami Da Aka Yi Wa Kisan Gilla Aiki
Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya shaida wa BBC cewa kisan da aka yi wa malamin ta’addanci ne kuma al’ummar Musulmi na bukatar a yi musu adalci.
Ya ce “A duk lokacin da aka rasa wani malami jigo, to an yi babbar asara ga al’umma baki daya.”
Sheikh Bala Lau, ya ce abin takaicin shi ne hanyar da aka bi wajen kisan malamin, domin hanya ce da kowanne musulmi zai nuna bakin cikinsa da alhininsa kan abin da aka aikata don kisan gilla ne.
Ya ce “Mu a matsayinmu na wannan kungiya, muna kira ga gwamnatin tarayya a kan ta dauki mataki wurin gano da kuma daukar mataki kan wadanda suka aikata wannan ta’addanci kuma mene ne manufarsu? Kuma me ake so a jefa wa alumma?”.
Sheikh Bala Lau ya ce “Wannan kisa ba za mu bari ba kuma ba za mu yi shiru ba za mu ci gaba da neman hakkin wannan malami.”
Shugaban kungiyar Izalar ya ce suna so a dauki matakin da ya dace bisa la’akari da dokokin kasa da kasa.