Asusun Bunkasa Aikin Noma na Kasa (NADF), ya ware Naira biliyan 19.5, domin samar da garabasar kashi 50 cikin 100, kan Irin noma da takin zamani da kuma maganin feshe.
A cewar Asusun ya yi haka ne, domin sama wa manoma kimanin 50,000 sauki, wanda za a gudanar a karkashin shirin kara habaka aikin noma na kasa.
- Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
- “Sin Daya Tak A Duniya”, Matsaya Ce Da Al’ummun Duniya Suka Kafe Kai Da Fata a Kai
An zabo amfanin gona hazu ne da suka hada da; Shinkafa, Masara, Rogo da kuma Waken Suya.
Kazalika, za a gudanar da shirin ne a daukacin shiyoyi shida na fadin wannan kasa.
A jawabinsa a wajen kaddamar da aikin, wanda aka gudanar a a babban birnin tarayyar Abuja, Babban Daraktan Asusun, Mohammed Abu Ibrahim ya bayyana cewa; an tsara shirin ne, musamman domin tallafa wa manoman kasar nan da kara samar da wadataccen abinci a kasar da kuma kara habaka tattalin arzikin kasar baki-daya.
Ya kara da cewa, Asusun ya kuma gano fannonin aikin noman kasar da ya kamata a kara bunkasa su, wanda hakan ya sanya Asusun ya dauki wannan mataki.
Ya ci gaba da cewa, duba da irin amfanin gonar da manoma ke nomawa a kasar, musamman kananan manoma da kuma ribar da suke samu daga fannin, wani abu ne da Asusun ya dauka da ke da matukar muhimmanci, wanda kuma hakan ne ya kara bai wa Asusun kwarin guiwar shirin fara kaddamar da aikin.
Shi kuwa a nasa jawabin, Lanre Wilton-Wadell, mai taimaka wa Babban Sakataren a Asusun, ya yi bayani kan yadda za a gudanar da aikin.
Ya bayyana cewa, Asusun zai bayar da kashi 100 na Irin noma da takin zanani da kuma magungunan feshi, wanda za a gudanar a karkashin shirin aikin noma na kasa.
Ya ci gaba da cewa, bayan an girbe amfanin gonar, Asusun zai biya wadanda suka sarrafa amfanin gonar kashi 50 cikin 100 na jimillar kayan aikin noman da aka kashe kudade a kansu.
“Mun fito da wannan shiri ne, duba da cewa; ana samun rarrabuwa a kasuwannin kasar da kuma samar da dama ga masu sarrafa amfanin gona tare da kara habaka amfanin da manoman kasar ke nomawa,” in ji Lanre.
“Mun yi duba a kan hanyar da zamu tabbatar da mun hada manoma, yadda za su samu damar kai amfanin da suka noma zuwa kasuwanni kai tsaye tare kuma da samun damar ci gaba da sarrafa amfanin gonar da aka girbe,” a cewar Lanre.
Ya bayyana cewa, kashi 70 cikin 100 na manoman kasar, musamman kanannan manoma na fuskantar kalubalen ilimi, kan ingantaccen Irin noman da ya kamata su yi amfani da shi da kwarewar aikin noma.
Kazalika, ya sanar da cewa; su ma masu sarrafa amfanin gonar, ba sa iya samun ci gaba da samun amfanin da za su sarrafa, saboda ayyuakan masu tare manoman suna saye amfanin da suka noma a farashi mai sauki
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp